PDP ta yi gayya ta ziyarci Gwamnan jihar Zamfara domin ta hana shi komawa Jam’iyyar APC

PDP ta yi gayya ta ziyarci Gwamnan jihar Zamfara domin ta hana shi komawa Jam’iyyar APC

- Gwamnoni da wasu Sanatocin jam’iyyar PDP sun zauna da Bello Matawalle

- Jiga-jigan Jam’iyyar hamayyar su na kokarin hana Gwamnan komawa APC

- Kafin yanzu manyan Gwamnonin APC sun gana da Gwamnan jihar Zamfara

Gwamnoni shida na jam’iyyar PDP, da Sanatoci, da wasu manyan ‘yan siyasa sun kai wa gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ziyara.

Jaridar Daily Trust ta ce makasudin ziyarar shi ne a hana gwamnan koma wa jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda ake rade-radin ya na shirin yi.

Gwamnonin jihohin da su ka taka kafa a Gusau jiya sun hada da: Seyi Mankinde (Oyo), Darius Ishaku (Taraba), da kuma Nyesom Wike (Ribas).

KU KARANTA: An yi wa Jagororin APC ihu a taron Jam’iyya a Kaduna

Ragowar gwamnonin su ne: Bala Mohammed (Bauchi), Umaru Fintiri (Adamawa) da Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto), wanda ya jagoranci tagawar.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnonin APC sun zauna da Bello Matawalle bayan gobarar da aka yi a kasuwar Gusau, har su ka ba gwamnan gudumuwar N50m.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa gwamnonin APC da Mai Mala Buni ya jagoranta sun yi wa Bello Matawalle tayin sauya-sheka zuwa jam’iyyarsu.

Wannan karo gwamnonin PDP sun ba gwamnatin jihar Zamfara gudumuwar kudi har N100m, kamar yadda gwamnan Sokoto, Waziri Tambuwal ya bayyana.

KU KARANTA: Gwamna Bala ya gayyaci Jonathan zuwa jihar Bauchi

PDP ta yi gayya ta ziyarci Gwamnan Zamfara domin ta hana shi komawa Jam’iyyar APC
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
Source: Twitter

Waziri Tambuwal ya ce akwai siyasa game da zuwan gwamnonin APC jihar, ya ce gwamnonin su na amfani da halin da ake ciki, su na yada manufarsu.

Gwamnan jihar Sokoto yake cewa: “Gwamnatin tarayya ba za ta iya ba mu tsoro ba, Zamfara gida ce, babu wani bako da zai iya korar ‘dan masu gida.”

A jawabinsa, Gwamna Bello Matawalle ya ce ‘yan PDP sun zo neman afuwa ne, kuma ya yafe masu.

A bangare guda, ku na labari cewa APC ta karamar hukumar Ahoada, jihar Ribas ta ba Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Abe watanni 3 su sasanta.

Jam'iyyar APC ta bukaci Ministan tarayyar da babban abokin fadansa, tsohon Sanatan Ribas su yi sulhu ko kuma a dauki matakin da ya dace a kansu.

Source: Legit

Online view pixel