Rikicin APC: Jam’iyya ta taso Amaechi da Sanata Abe a gaba, ta nemi su dinke barakarsu

Rikicin APC: Jam’iyya ta taso Amaechi da Sanata Abe a gaba, ta nemi su dinke barakarsu

- Jam’iyyar APC ta ba Rotimi Amaechi da Magnus Abe watanni 3 su yi sulhu

- An dade ana samun sabani tsakanin Ministan sufuri da tsohon Sanatan Ribas

- Jigon APC a Ahoada, Ibiso Nwuche, ya na barazanar hukunta ‘Yan siyasar

Jam’iyyar APC ta reshen karamar hukumar Ahoada, jihar Ribas ta ba Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Abe watanni su yi wa kansu sulhu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa APC ta bukaci Ministan tarayyar da abokin fadansa, tsohon Sanatan Ribas su sasanta, ko a dauki matakin da ya dace a kansu.

Jagoran APC na karamar hukumar Ahoada ta gabas, Ibiso Nwuche, ya bayyana cewa sun bada wa’adin ne saboda an gagara shawo kan manyan ‘yan siyasar.

KU KARANTA: Allah ya yi wa direban Shugaban Najeriya Buhari rasuwa

Mista Ibiso Nwuche ya yi magana ne bayan wani babban taro da APC ta shirya a karamar hukumar.

“Ganin babu abin da jam’iyyarmu ta amfana da shi saboda gazawar su a jiharmu da karamar hukumar Ahoada ta gabas, mun ba su zuwa watan Yuli su sasanta.”

“Su yi sulhu domin jam’iyya ta cigaba, ko kuma mu dauki mataki na gaba.” Inji Ibiso Nwuche.

Jagoran jam’iyyar ya kuma soki kalaman da Ministan yake yi na cewa bangaren da su ke cikin ruwa su fara shirin fito da gwamnan jihar Ribas a zaben 2023.

Rikicin APC: Jam’iyya ta taso Amaechi da Sanata Abe a gaba, ta nemi su dinke barakarsu
Magnus Abe da Rotimi Amaechi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Atiku Abubakar bai da damar neman kujerar Shugaban kasa –AGF

A cewar Ibiso Nwuche, kalaman da tsohon gwamna Rotimi Amaechi yake yi, ra’ayin kansa ne kurum yake fada, ba ya na magana ba ne da yawun jam’iyyar APC.

Nwuche ya bayyana cewa mutanen yankin Ekeye za su bayyana kudirinsu na neman takara a 2023, ya yi kira ga Ministan ya kyale ‘yan jam’iyya su tsaida zabinsu.

A baya kun ji cewa yiwuwar barin Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ta kara karfi bayan ya hadu da wasu Gwamnonin APC a garin Gusau a ranar Lahadin nan.

Gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi; Mala Buni, Badaru Abubakar, da Atiku Bagudu, sun fake da ‘gobara’, sun je sun yi maganar jawo Matawalle zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel