Gurgu ya hargitsa gangamin APC, ya yi wa Shugaban karamar hukuma ihun ‘Ba mu so’

Gurgu ya hargitsa gangamin APC, ya yi wa Shugaban karamar hukuma ihun ‘Ba mu so’

- Wani gurgu ya yi wa Shugabannin jam’iyyar APC ihun ‘ba mu so’ a taro

- Matashin ya shigo tsakiyar wajen taro ya soki shugaban karamar hukuma

- Ana zargin wannan ya faru ne a taron APC a garin Tudun-Wada a Zaria

Wani bidiyo ya zagaye kafofin yada labarai inda aka ga wani Bawan Allah ya na yi wa shugabannin jam’iyyar APC ihun bore da rana-tsaka.

Wani wanda ake kira Kwankwason Twitter shi ne ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Twitter.

Yayin da ake shirin kiran shugaban karamar hukuma ya yi jawabi, sai wannan mutumi da gurgu ne ya zaburo, ya fara yi masa ihun cewa ba su son shi.

KU KARANTA: Saboda na fadi zabe, na nemi wasu Mukarrabai na, na rasa – Jonathan

Wannan mutum gurgu ne wanda yake tafiya da sanduna, amma ya yi ta-maza ya shigo tsakiyar taro, ya na sukar shugaban karamar hukumar mai-ci.

Za a ji gurgun ya na cewa: “Karya ne, ba mu yi! Me ya yi mana wannan! Makaryaci ne wannan. Babu abin da ya yi mana. Ba mu so. Ba mu son shi…

Alamu sun nuna cewa wannan lamari ya faru ne a lokacin kaddamar da ‘dan takarar shugaban karamar hukuma wanda ya ke mulki a jam’iyyar APC.

Mabiya shafukan sada zumunta na zamani sun bayyana cewa wannan abin kunya ya faru ne a garin Tudun-Wada, karamar hukumar Zaria, jihar Kaduna.

KU KARANTA: Ana ta rufe kotu a garuruwa saboda Ma’aikatan shari’a su na yajin-aiki

Jam’iyyar APC mai mulki ce ta ke shugabancin karamar hukumar Zaria, kuma ana sa ran za ayi zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli a watan Yuni.

A cewar wani Bawan Allah, sunan wannan gurgu Ahmad, wanda ake kira da ‘Dudu’ a Tudun-Wada.

Wasu wanda su ka san wannan gurgu sun ce fitaccen ‘dan takife ne maras tsoro, kuma da ace ya na da kafafu, da watakila sai ya yi gigin marin ‘yan siyasa.

Kwanaki kun ji gwamnatin jihar Kaduna ta ce idan aka kama mutum ya yi magana da masu garkuwa da mutane da nufin biyan fansa zai dandana kudarsa.

Iyayen yaran da aka sace a Afaka sun yi tir da matakin da Gwamnatin Kaduna ta dauka, sun nuna a shirya su ke su biya kudi domin a fito masu da 'ya 'yansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng