Gwamna Bala ya gayyaci Jonathan zuwa Bauchi, Sarki ya ba tsohon Shugaban kasa sarauta

Gwamna Bala ya gayyaci Jonathan zuwa Bauchi, Sarki ya ba tsohon Shugaban kasa sarauta

- Sanata Bala Mohammed ya gayyatto Goodluck Jonathan zuwa jihar Bauchi

- Tsohon Shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya kaddamar da wasu ayyuka

- Gwamnan Bauchi ya yaba wa mutumin da ya fito da shi a siyasar Najeriya

Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yaba wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a kan ba shi mukami da ya yi a 2010.

A 2010 Goodluck Jonathan ya nada Bala Mohammed a matsayin Ministan birnin tarayya Abuja duk da a lokacin Sanatan ya na jam’iyyar adawa ta ANPP.

Bala Mohammed ya yi wannan bayani ne a lokacin kaddamar da wasu ayyuka da ya yi a Bauchi.

KU KARANTA: Ba za a taba cin ma burin kafa kasar Biyafara ba – Onochie

The Cable ta ce Gwamnan ya gayyaci tsohon shugaban kasar zuwa garin Bauchi domin ya kaddamar da aikin hanyoyin da ya yi a ranar Talatar nan.

A wajen wannan taro, Sanata Mohammed ya bayyana irin alakarsa da tsohon shugaban kasar wanda ya ce shi ne ya fito da shi fili a siyasar Najeriya.

Ya ce: “Mutumin da babu abin da ya hada ni da shi bayan zaman mu ‘yan kasa guda da kishin Najeriya, ya nada ni Ministan Abuja, ba tare da sani na ba.”

Gwamnan ya kara da cewa: “Kuma jam’iyyarmu daban-dabam.” Wannan bai hana Goodluck Jonathan ya ba Bala kujerar Minista mai tsoka a gwamnati ba.

Gwamna Bala ya gayyaci Jonathan zuwa Bauchi, ya fadi alherin da tsohon Shugaban kasa ya yi masa
Tsohon Shugaban kasa Jonathan a Bauchi Hoto: twitter.com/GEJonathan
Asali: Facebook

KU KARANTA: SWAGA ta na yi wa Tinubu yakin neman zaben Shugaban kasa

Da yake jawabi, Mohammed ya yabi tsohon shugaban Najeriyar game da yadda ya mika mulki bayan ya fadi zabe ba tare da ya jawo an yi wani rikici ba.

Jaridar ta bayyana cewa an sanya wa titin Sabon Kaura zuwa Miri sunan tsohon shugaban kasar. Jonathan ya ji dadin irin wannan girmama wa da aka yi masa.

Har ila yau Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu, ya ba Jonathan sarautar Jigon Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel