Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000

Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000

- Allurar rigakafin Covishield da ƙasar Indiya ta yi ma Najeriya alƙawarin kawo wa a matsayin gudummuwa ta iso Najeriya

- Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a taron da kwamitinsa ya saba yi duk sati

- Mustapha ya ce suna fatan yiwa 70% na yan Najeriya allurar rigakafin a cikin shekaru biyu masu zuwa

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar COVID19 (PTF) kuma sakataren gwamnatin tarayya, Mr Boss Mustapha, ya ce allurar rigakafin korona ta 'Covishield' guda 100,000 ta iso Najeriya daga ƙasar India.

KARANTA ANAN: Dukiyar Aliko Dangote, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu ta karu da Naira Tiriliyan 2 a 2021

Mustapha ya bayyana haka ne ranar Talata ya yin taron kwamitin su a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ya kuma ƙara da cewa akwai sauran allurar rigakafin da zata iso Najeria nan gaba daga ƙungiyar ƙasashen Africa.

A jawabin da ya yi a wajen taron, Boss Mustapha ya ce:

"Kamar yadda kowa ya sani, An kawo allurar rigakafin Oxford/Astrazeneca Najeriya a ranar 2 ga watan Maris."

"Waɗannan rigakafin kashin farko ne daga cikin 16 miliyan da aka ware ma Najeriya daga shirin COVAX, ana bukatar a yi ma kaso 20% na yawan al'ummar ƙasar nan."

Rigakafin COVID19 ta Covishield 100,000 ta iso Najeriya daga ƙasar Indiya
Rigakafin COVID19 ta Covishield 100,000 ta iso Najeriya daga ƙasar Indiya Hoto: @NCDCgov
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin ya kuma ƙara da cewa akwai sauran rigakafin da yawa da zasu iso Najeriya daga ƙungiyar ƙasashen Africa.

Ya kuma ce akwai rigakafin Covishield da ta iso Najeriya guda 100,000 wadda gwamnatin Indiya ta baiwa Nijeriya gudummuwa.

KARANTA ANAN: CAN ta caccaki Buhari: Ba a zabe ka don kazo ka yi korafi kan shugabancin baya ba

A cewarsa wannan zai kara adadin waɗanda za'ayi ma allurar da mutum 50,000.

Mustapha ya ce kwamitinsa da ma'aikatar lafiya (FMoH), da hukumar kula da lafiya a matakin farko (NPHCDA) zasu fi maida hankali ne ga jami'an lafiya, shuwagabanni, da kuma waɗanda suka wuce shekara 50 wajen yima rigakafin a faɗin ƙasar nan.

Ya ce tun daga randa aka fara rigakafin zuwa ran 5 ga watan Afrilu, an yima yan Najeriya kimanin 963,802 allurar rigakafin a karon farko.

Ya ƙara da cewa suna fatan yi ma 70% na yan Najeriya rigakafin tsakanin 2021 zuwa 2022.

Wakilin ƙasar Indiya a Najeriya, Mr Velagaleti Surendra, ya mika wa shugaban kwamitin yaƙi da COVID19 ɗin allurar rigakafin da ƙasar sa ta kawo gudummuwa.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya gwangwaje yan kasuwar Jihar Katsina da Gudummuwar Kuɗi Miliyan N20m

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa gwamnatin Katsina da kuma yan kasuwar jihar bisa gobarar da ta faru a wata babbar Kasuwa a jihar.

Hakanan kuma gwamnan tare da yan kasuwar jihar Kano sun bada gudummuwar Naira 20 miliyan ga yan kasuwar da abun ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel