Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya bayyana babban abin da yake kashe Najeriya a yau

Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya bayyana babban abin da yake kashe Najeriya a yau

- Goodluck Ebele Jonathan ya ce ‘alfarma’ ta na jawo ci-baya a Najeriya

- Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka da ya kai ziyara zuwa Bauchi

- Jonathan ya ce lokacin da ya yi mulki, cancanta ya duba ba sanayya ba

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce son-kai da ake nuna wajen bada kujerar shugabanci ya na kawo wa kasar nan matsala.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Goodluck Jonathan ya koka game da yadda ake nuna alfarma, a zakulo ‘yan uwa da abokan arziki idan aka tashi bada mukami.

Da yake jawabi a fadar Sarkin Bauchi, Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana cewa rashin amfani da cancanta ne ya jefa kasar a halin da ta ke ciki yanzu na ci baya.

KU KARANTA: An karrama Goodluck Jonathan a jihar Bauchi, an ba shi sarauta

A ranar Talata, 6 ga watan Afrilu, 2021 ne Dr. Jonathan ya kai ziyara zuwa fadar Sarkin Bauchi.

Jonathan yake cewa a Najeriya kafin mutum ya samu mukami ko a daura masa wani nauyi, dole sai ya san wani babba a gwamnati, wanda hakan ya jawo ci-baya.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne bayan gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya ce bai san shi ba amma ya nada shi Ministan Abuja a gwamnatinsa.

“Kwarai, ban san shi ba a lokacin da mu ka hadu da shi, na nada shi Ministan tarayyar Abuja.”

KU KARANTA: Ba za a taba cin ma burin kafa kasar Biyafara ba – Hadimar Buhari

Jonathan a Bauchi Hoto: twitter.com/SenBalaMohammed
Jonathan a Bauchi Hoto: twitter.com/SenBalaMohammed
Asali: UGC

“Mu na da wannan ra’ayi na cewa mutane su na ganin akwai ma’aikatun da sun fi wasu tsoka don haka dole a ba wasu mutane na musamman ko wanda ka sani.”

Jonathan wanda ya sauka daga mulki a 2015 ya ce: “Ni ba haka na ke yi ba, ba haka na ke aiki na ba.”

A jawabinsa, tsohon shugaban na Najeriya ya bada labarin yadda wasu daga cikin hadimansa su ka kaurace masa bayan ya sauka daga kan kujerar shugaban kasa.

A ranar Talata kun ji cewa Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya ma hanyar sabon titin garin Ƙaura zuwa Mira sunan tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

Bayan haka, Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu da 'yan majalisar masarautar kasar Bauchi sun ba Jonathan sarauta yayin da ya kai ziyara zuwa jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel