Yawaitar hatsarin mota yasa Dangote ya kaddamar da cibiyar horar da direobi

Yawaitar hatsarin mota yasa Dangote ya kaddamar da cibiyar horar da direobi

- Duba da yawan hatsarin motocin Dangote, kamfanin ya kaddamar da cibiyar horar da direbobi

- Kamfanin na Dangote ya bayyana hakan a matsayin mafita ga yawan hadduran manyan motoci

- Kamfanin ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu cibiyar ta horar da direbobi sama da 50

Kamfanin Simintin Dangote ya kaddamar da Cibiyar Horar da Direbobi a Kamfanin Siminti na Dangote (DCP) dake Obajana, Jihar Kogi don magance hatsarin sufuri a hanyoyi, Daily Trust ta ruwaito.

Cibiyar ta kuma horar da direbobi 50 zuwa yanzu. A yayin taron kaddamarwar a karshen makon da ya gabata, Shugaban Cibiyar Horar da Direbobi, Mista Harisson Pepple, ya ce horarwar ta yi daidai da tsarin kamfanin na kin jinin hatsarin mota.

Mista Pepple ya ce an fitar da direbobin da suka samu horon ne daga samarin da suke da su, kuma lokacin ba da horon wata shida ne.

KU KARANTA: Rikicin addini a Gombe: Gwamna Yahaya ya tallafawa wadanda rikici ya rutsa dasu

Yawaitar hatsarin mota yasa Dangote ya kaddamar da cibiyar horar da direobi
Yawaitar hatsarin mota yasa Dangote ya kaddamar da cibiyar horar da direobi Hoto: paradisenews.ng
Asali: UGC

Ya nuna kwarin gwiwarsa da cewa "ranakun hatsarin da ya shafi manyan motocin Dangote sun kusa zuwa karshe".

“Shirin Horar da Direbobin ya game komai. Makonni goma sha biyu na farko zunzurutun karatu ne. Sannan watanni uku kuma a aikace,” inji shi.

Ya ce, an kirkiro wannan tunani ne na sabuwar Cibiyar Koyar da Direbobi, a watan Yunin shekarar 2020, da nufin horarwa, da sake horas da wasu, da kuma jan hankalin direbobin na Dangote.

Ya kuma sanar da cewa kamfanin yana da rukunin horar da kwararrun direbobi da basu lasisin Class G, yana mai jaddada cewa kamfanin na yin duk mai yiwuwa ne don kawar da kansa daga hadarurruka.

A cewarsa, kamfanin yana hada gwiwa da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a cikin mafi yawan ayyukanta, ya kara da cewa an kuma horar da direbobin da ke horar da dabarun tuki na kariya, wanda ya hada da tuki don ceton rayuka, lokaci da dukiya.

KU KARANTA: CAN ta caccaki Buhari: Ba a zabe ka don kazo ka yi korafi kan shugabancin baya ba

A wani labarin, Mujallar Forbes ta bayyana cewa dukiyar da manyan Attajiran Najeriya uku su ka mallaka ta karu da Dala biliyan 5.7 a cikin shekara daya tal.

Abin da Attajirai su ka mallaka a yanzu ya kai Dala biliyan 22.5. A kudin mu na gida, abin da ya karu a dukiyarsu ya haura Naira tiriliyan biyu.

Punch ta ce an fitar da jerin manyan masu kudin Duniya ne a ranar Talata, 6 ga watan Afrilu, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.