Dukiyar Aliko Dangote, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu ta karu da Naira Tiriliyan 2 a 2021

Dukiyar Aliko Dangote, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu ta karu da Naira Tiriliyan 2 a 2021

- Masu kudin Najeriya sun samu karin $5.7bn a cikin dukiyarsu a shekara guda

- Aliko Dangote, Mike Adenuga, da Abdussamad Rabiu sun samu makudan kudi

- A kudinmu na gida, Attajiran sun tashi ne da Naira tiriliyan 2.2 a shekarar bara

Mujallar Forbes ta bayyana cewa dukiyar da manyan Attajiran Najeriya uku su ka mallaka ta karu da Dala biliyan 5.7 a cikin shekara daya tal.

Abin da Attajirai su ka mallaka a yanzu ya kai Dala biliyan 22.5. A kudin mu na gida, abin da ya karu a dukiyarsu ya haura Naira tiriliyan biyu.

Punch ta ce an fitar da jerin manyan masu kudin Duniya ne a ranar Talata, 6 ga watan Afrilu, 2021.

KU KARANTA: Elon Musk ya na kan gaba a sahun fitattun Masu kudin 2021

Rahoton ya nuna dukiyar babban mai kudin nahiyar Afrika, Aliko Dangote ta karu daga dala biliyan $8.3 zuwa dala biliyan 11.5 a shekarar 2020.

Wannan kari na fiye da Dala biliyan uku (Naira biliyan uku) ya sa Dangote ya zama mutum na 191 a cikin jeringiyar attajiran da ake da su a Duniya.

Shugaban kamfanin Globacom da Conoil Plc, Dr. Mike Adenuga, shi ne attajiri na biyu a Najeriya, kuma na biyar a Afrika, sannan na 440 a fadin Duniya.

Arzikin Mike Adenuga ya karu daga Dala biliyan 5.6 zuwa Dala biliyan 6.1 a shekarar da ta wuce.

Dukiyar Aliko Dangote, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu ta karu da Naira Tiriliyan 2 a 2021
Aliko Dangote da Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jerin manyan attajiran da ake ji da su a Afrika

Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya samu karin Dala biliyan 2 a bara, karin na N800m ta sa ya zama na 574 a Duniya, na shida a Afrika

Sauran attajiran Afrika a wannan jeri sun kunshi mutane biyar daga kasar Afrika ta Kudu, masu kudi biyar daga Masar da wani mutumin kasar Aljeriya.

Kwanakin baya kun samu rahoto cewa wanda ke bayan Dangote shi ne Balaraben nan, Nassef Sawiris, wanda ya tada kai da fiye da fam Dala biliyan 8.3

Ragowar masu kudin nahiyar Afrikan su ne: Naguib Sawiris, Mohamed Mansour, Yasseen Mansour, Koos Bekker, Patrice Motsepe da Michiel Le Roux.

Asali: Legit.ng

Online view pixel