Gwamna Ganduje ya gwangwaje yan kasuwar Jihar Katsina da Gudummuwar Kuɗi Miliyan N20m

Gwamna Ganduje ya gwangwaje yan kasuwar Jihar Katsina da Gudummuwar Kuɗi Miliyan N20m

- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa gwamnatin Katsina da kuma yan kasuwar jihar bisa gobarar da ta faru a wata babbar Kasuwa a jihar

- Hakanan kuma gwamnan tare da yan kasuwar jihar Kano sun bada gudummuwar Naira 20 miliyan ga yan kasuwar da abun ya shafa

- Ganduje tare da shuwagabannin yan kasuwar Kano sun kai ziyara jihar ta Katsina don nuna alhinin su kan abun da ya faru a watan da ya gabata

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da yan kasuwar jihar Kano sun bada gudummuwar zunzurutun kuɗi 20 miliyan ga yan kasuwar jihar Katsina da gobara ta shafa kwanan nan.

KARANTA ANAN: Kubi Sahun mu ku shiga yajin aiki ko mu ciku tarar 5 Miliyan, NARD ta gargaɗi Likitocin COVID19

Gwamna Ganduje tare da shuwagabannin yan kasuwar jihar Kano sun je Katsina ranar Talata don yin jaje a kan abinda ya faru, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Tawagar gwamnan ta yi jaje ga gwamnatin jihar ta Katsina da kuma al'ummar jihar baki ɗaya kan wannan lamari mara daɗi na gobara da ta faru, wanda ya yi sanadiyar salwantar manyan dukiyoyi na biliyoyin nairori.

Gwamnan ya bayyana cewa sun zo ne tare da yan kasuwar jiharsa waɗanda suka nuna matukar damuwarsu akan lamarin da ya faru.

Gwamna Ganduje ya gwamgwaje yan kasuwar Jihar Katsina da Gudummuwar Kuɗi Miliyan N20m
Gwamna Ganduje ya gwamgwaje yan kasuwar Jihar Katsina da Gudummuwar Kuɗi Miliyan N20m Hoto: @Thenationnews
Source: Twitter

Gwamnan ya ƙara da cewa suma yan kasuwar mu sun fusakanci irin wannan ƙalubale a kasuwar Sabon Gari dake jihar Kano.

KARANTA ANAN: Sauyin Sheƙa: Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar

Gwamnan ya ce, saboda sanin irin ɗacin abun, munzo tare da su mu jajanta ma gwamnatin jiha da kuma mutanen jihar musamman waɗanda suka rasa dukiyoyinsu.

A jawabinsa, gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya yi ma gwamnan Kano da tawagarsa godiya a kan wannan gudummuwa da suka bayar.

In zaku iya tunawa a watan da ya gabata ne gobara ta tashi a babbar Kasuwa a jihar Katsina, inda gobarar ta yi sanadiyyar rasa dukiyoyi da dama.

A wani labarin kuma Abin da yasa Buhari bai bar tsohon IGP Adamu ya ƙarasa ƙarin wata 3 da ya masa ba, Ministan Ƴan Sanda

Mohammad Dingyadi, Ministan Yan Sanda ya yi magana game da nada sabon IGP Alkali Baba da Buhari ya yi.

Dingyadi, ya ce duk da cewa Shugaba Buhari ya kara wa tsohon IGP Adamu wa'addin wata 3, yana kuma da ikon nada sabo duk lokacin da ya ke so.

Source: Legit

Online view pixel