2023: Fitaccen dattijon kasar Yarbawa ya sa wa burin Jigon APC, Bola Tinubu albarka
- Kungiyar SWAGA ta kai wa Reuben Fasoranti ziyara a gidansa da ke Ondo
- Reuben Fasoranti ya nuna goyon baya ga takarar Bola Tinubu a zaben 2023
- Tsohon Shugaban Afeniferen ya na ganin Tinubu zai yi kyau da shugabanci
Tsohon shugaban kungiyar nan ta Afenifere, Reuben Fasoranti, ya ce jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya cancanci ya zama shugaban kasa a 2023.
Jaridar The Cable ta ce Reuben Fasoranti ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da kungiyar the South-West Agenda for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘ya ‘yan kungiyar ta SWAGA sun kai wa dattijon ziyara ne a garin Akure, Ondo a ranar ranar Talata, 6 ga watan Afrilu, 2021.
KU KARANTA: An yi wa tsofaffin 'Yan PDP wankan tsari bayan sun shigo APC
“Tinubu ya na da duk abin da ake bukata na shugabancin Najeriya. Idan aka yi la’akari da hidimarsa da aikin da ya yi, ya cancanci ya yi mulki a 2023.”
Reuben Fasoranti ya cigaba da cewa: “Ina rokon Ubangiji ya amsa masa addu’arsa, idan ya samu kujerar (shugaban kasa), zai yi duk abin da mu ke so.”
Dattijon ya ce idan har tsohon gwamnan na Legas ya samu shugabanci, za a biya wa kungiyar Afenifere bukata, musamman a maganar sauya fasalin kasa.
Ya ce: “Tinubu ya na da duk abin da ake bukata a mulki Najeriya, mutum ne maras nuna kabilanci, mai son talakawa, ga tarin hikima da yake da shi.”
KU KARANTA: Fani-Kayode ya fadi wanda ya kamata a zaba a 2023
Da yake jawabi, shugaban kungiyar SWAGA mai goyon-bayan Bola Tinubu ya tsaya takara, Sanata Dayo Adeyeye, ya ce dole Yarbawa su hada-kai kafin zaben 2023.
Tsohon Ministan ayyukan na Najeriya ya ce kawo yanzu, SWAGA ta kai wa Sarakuna fiye da 50 ziyara a jihohi shida da ake da su a yankin Arewa maso yamma.
Kun ji cewa jam'iyyar APC ta ba Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Sanatan da su ke rikici watau Magnus Abe watanni 3 su yi sulhu ko kuma a hukunta su.
Ganin an dauki tsawon lokaci an gagara shawo kan Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Abe a jihar Ribas, APC ta ce za ta hukunta manyan 'yan siyasar na ta.
Asali: Legit.ng