2023: Tsohon Minista Fani-Kayode ya fadi wanda ya kamata ya zama 'Magajin Buhari'

2023: Tsohon Minista Fani-Kayode ya fadi wanda ya kamata ya zama 'Magajin Buhari'

- Tsohon Minista Femi Fani-Kayode ya ba ‘Yan Najeriya shawarar wanda za a zaba

- Femi Fani-Kayode ya yi kira ga al’umma su goyi bayan matashi ne a zabe mai zuwa

- Jagoran adawar ya gargadi jama’a a kan zaben ‘dan takarar da bai san kan aiki ba

Tsohon Ministan harkokin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode, ya yi kira ga mutanen Najeriya su zabi matashin shugaban kasa a 2023.

Da yake dogon jawabi a shafinsa na Twitter, @realFFK, Femi Fani-Kayode ya bada shawarar a zabi shugaban kasa mai matsakaicin shekaru a Najeriya.

Fani-Kayode ya ce a halin yanzu gwagwarmayar da ake yi a siyasar kasar nan ta zarce batun jam’iyyar APC mai mulki da jam’iyyar PDP mai hamayya.

KU KARANTA: Atiku Abubakar bai da damar neman kujerar Shugaban kasa – AGF

Cif Fani-Kayode ya nemi mutanen kasar nan su zabi ‘dan takarar da ya fi cancanta, ba tare da la'akari da jam'iyyar da ya tsaya a kai ba, FFK ya ce:

“Ku yi zabi da kyau, ku tabbatar kun yi nazari sosai, ku fahimci kowane bangare. Dalili kuwa shi ne idan aka yi zaben tumin dare zai shafi kowa da kowa.”

“Idan mu ka zabi matashi, mai karfi, mai daukar mataki, jajirtacce, kai-tsaye, mai tunani, maras nuna kabilanci, mai tsayawa inda ya dace, mai tausayi da hada-kan al’umma, mun yi abin da ya dace.”

Jagoran na PDP ya ce za a yi kuskure idan aka zabi akasin haka:

KU KARANTA: APC ta ba Amaechi da Abe watanni 3 su yi sulhu ko a hukunta su

“Amma kuma idan mu ka yi kuskuren zaben maras imani, wanda bai san aiki ba, maras basira, wanda neman mulki da dukiya kurum ke gabansa, bai san halin da ake ciki ba, mai fama da cutar mantuwa, ya ki yarda da barakar da ake ciki.”

Ya ce zabin da ke gaban ‘Yan Najeriya a 2023 tsakanin masu neman a barka kasar nan ne da kuma wadanda su ke kokarin ganin an dinke an cigaba da zama daya.

FFK ya ja-kunnen mutane game da zaben wadanda ba su da wani buri illa su dare kan mulki su tara dukiya, ya ce wadannan ba su da niyyar hada-kan al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng