Fusatattun matasa sun zane matasan da suka yi zanga-zangar kin Buhari a Kogi

Fusatattun matasa sun zane matasan da suka yi zanga-zangar kin Buhari a Kogi

- Fusatattun matasa a jihar Kogi sun zane waus matasa ciki da baya bayan sun fito zanga-zangar kin Buhari

- An umarcesu da su goge duk wasu rubuce-rubece da suka yi na 'Buhari Must Go' da suka yi a bango

- Ana tsabga musu bulalai suna ratsa mazaunansu yayin da suke goge rubutun a bango da sauran wurare

Wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda aka ga wasu matasan jihar Kogi dauke da bulalai suna tsabga wa wasu matasa biyu da suke zanga-zangar nuna kiyayya ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A bidiyon wanda Premium times ta wallafa a ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu an ga matasan suna cire 'Buhari Must Go' daga jikin bango ana basgarsu da bulalai a mazaunansu.

Sun umarci matasan da su sake yin fenti a bango yayin da suke shan ruwan bulalai.

Alamu sun nuna cewa har yanzu matasan jihar Kogi suna goyawa Shugaba Buhari baya. A cikin bidiyon, an ji wani matashi da yake dukan masu zanga-zangar yana cewa 'jihar Kogi ta Buhari ce'.

KU KARANTA: Da duminsa: An tsinci jirgin yakin sojin saman Najeriya a wajen Maiduguri

Fusatattun matasa sun zane matasan da suka yi zanga-zangar kin Buhari a Kogi
Fusatattun matasa sun zane matasan da suka yi zanga-zangar kin Buhari a Kogi. Hoto daga Premium Times
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Tsohon mukaddashin gwamnan jihar Delta, Sam Obi, ya rasu

Legit.ng ta tattaro cewa bidiyon Kogi ya bayyana ne bayan sa'o'i kadan da magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun taru a gaban gidan gwamnatin Najeriya dake London don nuna kara ga shugaban kasan.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter a ranar Litinin inda ya kwatanta masu goyon bayan Buhari da 'yan kasa nagari.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma'aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

"A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba," cewar Ngige.

Asali: Legit.ng

Online view pixel