Yan Ƙasar China da aka Sace Makon da ya gabata a Ogun Sun kuɓuta

Yan Ƙasar China da aka Sace Makon da ya gabata a Ogun Sun kuɓuta

- Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ta tabbatar da sakin wasu yan asalin ƙasar China su biyu da aka sace satin daya gabata sun samu kuɓuta daga hannun yan fashi

- A ranar Laraban makon da ya gabata ne wasu yan bindiga da ba'asan ko suwaye ba suka farmaki mutanen biyu a cikin gonarsu a garin Oba, kuma suka tafi dasu zuwa inda ba'a sani ba

- Mai magana da yawun yan sanda ya tabbatar da sakin mutanen biyu sai dai bai bayyana ainihin cewa an biya kuɗin fansa kafin sakin nasu ko a'a

Wasu yan ƙasar China su biyu da aka sace daga gonarsu a garin Oba dake ƙaramar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun a makon da ya gabata sun kuɓuta.

KARANTA ANAN: Ganduje ya zabtare rabin albashinsa da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa

Rahotanni sun bayyana cewa an sace mutanen biyu ne daga gonakinsu ranar Laraban satin da ya gabata.

Wakilin jaridar Dailytrust ya gano cewa an bada wasu kuɗaɗe da sunan kuɗin fansa, amma bai iya gano ko nawa aka bayar ɗin ba.

Labari Mai Daɗi! Yan Ƙasar China da aka Sace Makon da ya gabata a Ogun Sun kuɓuta
Labari Mai Daɗi! Yan Ƙasar China da aka Sace Makon da ya gabata a Ogun Sun kuɓuta Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Yan bindigar da suka sace yan ƙasar China ɗin sun shigo gonar tasu ne ta hanyar Rafin Ogun, kuma sun tsere da mutanen ne ta wannan hanyar da suka shigo.

Mai magana da yawun yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sakin mutanen biyu yan asalin ƙasar China.

KARANTA ANAN: Abin da yasa Buhari bai bar tsohon IGP Adamu ya ƙarasa ƙarin wata 3 da ya masa ba, Ministan Ƴan Sanda

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda aka sace ɗin sun samu kuɓuta ne bayan wani namijin ƙoƙari da jami'an yan sanda suka yi don ganin sun kuɓutar da su.

Sai dai, mai magana da yawun yan sandan baice komai a kan ko anbiya wasu kuɗaɗe kafin a sake su, ko kuwa yan bindigar sun sake su ne bisa ra'ayin kansu.

A wani labarin kuma Matashin da ya aura mata 2 a rana daya ya bada labarin romon amarcin da yake kwasa

Dan Najeriyan nan da ya auri mata biyu a rana daya ya bayyana yadda al'amura suke gudana a gidansa a halin yanzu.

Mutumin mai shekaru 37 yace duk wasu abubuwa na so da kauna da yake samu suna nunkuwa ne kullum.

Source: Legit.ng

Online view pixel