Abin da yasa Buhari bai bar tsohon IGP Adamu ya ƙarasa ƙarin wata 3 da ya masa ba, Ministan Ƴan Sanda

Abin da yasa Buhari bai bar tsohon IGP Adamu ya ƙarasa ƙarin wata 3 da ya masa ba, Ministan Ƴan Sanda

- Mohammad Dingyadi, Ministan Yan Sanda ya yi magana game da nada sabon IGP Alkali Baba da Buhari ya yi

- Dingyadi, ya ce duk da cewa Shugaba Buhari ya kara wa tsohon IGP Adamu wa'addin wata 3, yana kuma da ikon nada sabo duk lokacin da ya ke so

- Ministan 'yan sandan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a gidan gwamnati

Mohammad Dingyadi, Ministan 'Yan Sanda a Nigeria, ya yi magana kan dalilan da yasa Mohammed Adamu, tsohon sufeta janar na 'yan sandan Nigeria bai kammala karin wa'adin watanni uku da aka yi masa ba, rahoton The Cable.

Ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da ikon yin sabon nadi a lokacin da ya ke so.

Abin da yasa Buhari ya sauke tsohon IGP Adamu kafin wa'adin da ya masa ya cika, Ministan 'Yan Sandan
Abin da yasa Buhari ya sauke tsohon IGP Adamu kafin wa'adin da ya masa ya cika, Ministan 'Yan Sandan. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Shugaba kasar ya amince da nadin Alkali Usman Baba a matsayin sabon IGP na yan sanda.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Baba ya maye gurbin Adamu wanda shugaban kasar ya yi wa karin wa'addin watanni uku a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021. Adamu ya yi watanni biyu da kwanaki uku cikin wa'adin watanni ukun da aka bashi da farko.

Yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a gidan gwamnati, an yi wa ministan yan sandan tambaya kan dalilin da yasa shugaban kasar bai bari karin wa'adin da ya yi wa IGP mai barin gado ya kare ba.

A martaninsa, ya ce: "Shugaban kasa ya san da hakan kuma ba za ka iya dauke wannan nauyin daga gare shi ba; shine ke da ikon yin nadi ko yin karin wa'addi.

"Yanzu kuma ya zabi ya nada sabon mutum. Don haka ku kyale shi domin huruminsa ne shi kadai kuma babu abin da za ku iya yi a kan hakan."

KU KARANTA: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Dingyadi ya ce shugaban kasar ya godewa IGP mai barin gado 'bisa jajircewa da kwarewar aiki da ya nuna yayin zamaninsa."

Da ya ke tsokaci kan sabon shugaban yan sandan, ministan ya ce an zabe shi ne bisa cancanta cikin sauran jami'an rundunar masu mukamin DIG da AIG da za a iya nadawa matsayin IGP.

Ya kara da cewa shugaban kasa ya bukaci Baba ya tashi tsaye ya tunkari babban kalubalen da ke gabansa na samar da tsaro a kasar da inganta tsarin tsaro a kasar.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel