An yi an gama, ‘Yan Kudu ba za su taba ballewa su kafa Biyafara ba kuma inji Hadimar Buhari

An yi an gama, ‘Yan Kudu ba za su taba ballewa su kafa Biyafara ba kuma inji Hadimar Buhari

- Lauretta Onochie ta tsoma baki game da fafukar kafa kasar Biyafara

- Hadimar shugaban Najeriyar ta ce babu maganar Biyafara har abada

- Onochie ta ce gwagwarmayar ballewa daga Najeriya ta kare tun 1970

Daya daga cikin hadiman shugaban kasar Najeriya, Lauretta Onochie, ta fito ta na cewa ba za a taba samar da kasar Biyafara ba.

Misis Lauretta Onochie wanda ta ke ba shugaban kasa shawara kan dandalin sada zumunta na zamani ta ce fafutukar Biyafara ta kare.

Lauretta Onochie ta bayyana wannan ne a shafin ta na Twitter a ranar Litinin, 5 ga watan Afrilu, 2021.

KU KARANTA: IGP ya bada umarni a koyawa 'Yan IPOB hankali

A cewar Lauretta Onochie, fafutukar mutanen Kudu na balle wa daga Najeriya ta zo karshe ne a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon.

Onochie take cewa gwagwarmayar ta kare a ranar da Janar Philip Effiong ya jagoranci dakarunsa, su ka sallama wa gwamnatin Najeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara ta wallafa wani bidiyo da ya nuna Manjo-Janar Philip Effiong ya na mika kai a madadin sojojin Biyafara.

Philip Effiong shi ne mataimakin shugaban kasar Biyafara da aka nemi a kafa tsakanin 1967 da 1970.

KU KARANTA: Dokubo Asari ya kafa sabuwar tafiyar ‘Yan Biyafara

An yi an gama, ‘Yan Kudu ba za su taba ballewa su kafa Biyafara ba kuma inji Hadimar Buhari
Lauretta Onochie Hoto: @Laurestar/Twitter
Asali: UGC

“Hankalin Philip Effiong, mataimakin Janar Ojukwu (Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu) a lokacin da shi da sojojinsa su ka mika wuya."

Hadimar ta cigaba, "Effiong ya na cewa #NeverAgainBiafra, fuskar shugaban kasa na wancan lokacin Yakubu Gowon, ya nuna cewa #OneNigeria."

Wannan Baiwar Allah ta karkare maganar ta da: "A wannan lokaci ne aka birne yunkurin kafa kasar Biyafara. Ba za a taba samun Biyafara ba. Har abada."

Dazu kun ji Femi Fani-Kayode ya fito ya na cewa Idan 2023 ta zo, ba batun Jam’iyyar APC da PDP za ayi ba, ya bada shawarar a zabi 'dan takarar da ya dace.

Gawurtaccen ‘Dan adawar ya fara kiran mutane su yi watsi da APC da PDP a 2023. Wannan kira na shi ya zo daidai da na tsohon Gwamna Rochas Okorocha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel