Ba zamu iya biyanku Cikakken Albashin Watan Maris ba, Ganduje ya faɗawa ma'aikata
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba zata iya biyan ma'aikatan jihar cikakken albashin su na watan Maris ba
- Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Malam Muhammad Garba ne ya faɗi haka, a cewarsa babu kuɗi a asusun gwamnatin jihar da zasu isa a biya albashin
- Sai dai a ɓangaren ma'aikatan kuwa, ƙungiyar ƙwadugo reshen jihar ta baiwa gwamnatin wa'adin mako ɗaya ta biya dukkan ma'aikatan jihar albashinsu
Gwamnatin jihar Kano ta ce bazai yuwu ta biya ma'aikatan jihar cikakken albashin su na watan Maris ba, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Gwamnatin, ta bakin kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya jingina haka da saukar kuɗin da suke samu daga gwamnatin tarayya.
KARANTA ANAN: Yajin aiki: Minista Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa
Kwamishinan ya ce kashin da gwamnatin jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya ya sauka, wanda bayan nazari akansa suka gano zai yi matuƙar wahala gwamnatin jihar ta iya biyan sabon tsarin albashi.
Sai dai, duk da haka ƙungiyar ƙwadugu ta jihar (NLC) ta baiwa gwamnatin wa'adin kwanaki bakwai ta maida ma ma'aikatan ragowar albashin su.
Kuma NLC ta bayyana rage kuɗin albashin ma'aikatan da gwamnatin ta yi da cewa ya saɓa ma doka.
Shugaban NLC reshen jihar ne ya bayyana bada wa'adin jim kaɗan bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da ƙungiyar suka yi.
Shugaban ya ce, matuƙar gwamnatin bata dakatar da wannan rage albashin ba har wa'adin ya kare, to ma'aikatan zasu tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana uku.
Da yake maida martani kan lamarin, kwamishinan yaɗa labaran jihar ya ce, shiga yajin aikin bazai warware matsalar ba.
Malam Garba ya ce, a watan maris gwamnatin jihar ta karɓi N12,400,000,000 daga asusun gwamnatin tarayya.
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga dauke da AK47 sun budewa jigon APC wuta a jihar Delta
A cikin waɗannan kuɗaɗen akwai N6,100,000,000, kason gwamnatin jihar da kuma N6,300,000,000 kason kananan hukumomi 44 da jihar ke da su.
Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jiha na buƙatar ƙarin biliyoyin nairori kafin ta iya biyan Albashin ma'aikatan jihar, wanda a yanzun babu kuɗin da za'a ƙara ɗin.
A cewar kwamishinan, taron da suka yi da ƙungiyar ƙwadugon jihar a watan Mayun shekarar data gabata, sun cimma matsayar biyan ma'aikata albashi bisa yadda jihar ta samu daga asusun ƙasa.
Ya kuma yi kira ga ƙungiyar ƙwadugon da kuma sauran ma'aikatan jihar da su nuna goyon bayansu don cigaba da gina kyakkyawar alaƙa tsakaninsu da gwamnati.
Daga ƙarshe, kwamishinan ya tabbatarwa da ma'aikatan jihar cewa zasu cigaba da samun cikakken albashinsu da zarar wannan matsalar ta kauce.
A wani labarin kuma Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno
A tsakar daren Lahadi 'yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa sansanin sojoji farmaki.
Majiyoyi da dama sun tabbatar da yadda 'yan Boko Haram suka yi musayar wuta da sojojin.
Asali: Legit.ng