JIBWIS ta yi kira ga Gwamnatin shugaba Buhari da ta ƙara ƙaimi a yakin da take da yan ta'adda
- Ƙungiyar Addinin musulunci JIBWIS ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi wa Allah ta ƙara ƙaimi a yaƙin da take da yan ta'adda
- Ƙungiyar ta faɗi haka ne a ya yin rufe taron ƙara ma juna sani da ta saba shiryawa duk shekara karo na 28
- Shugaban Majalisar malamai na ƙungiyar, Sheik Sani Yahaya Jingir, ya yi wannan kiran a wajen taron wanda aka yi wa laƙabi da 'Manhagar addinin musulunci kan taɓarɓarewar zaman lafiya da cigaba a faɗin Duniya
Ƙungiyar addinin musulunci ta JIBWIS ta yi kira ga gwamnatin shugaba Buhari da ta ƙara ƙaimi a kan yaƙin da take da yan fashi da makami da sauran ire-iren ta'addanci da suka addabi ƙasar nan.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda ta sheƙe yan garkuwa da mutane a wani Batakashi da suka yi
JIBWIS ta yi wannan kira ne ta hannun shugaban majalisar malamai na ƙungiyar, Sheik Sani Yahaya Jingir, a wajen taron ƙara ma juna sani da ƙungiyar ta saba shiryawa, karo na 28.
Tawagar ƙungiyar ta ce abun takaici ne irin halin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki, wanda idan ba'a ɗauki matakin da ya dace ba to ƙasar zata shiga cikin halin ƙaƙani-kayi.
A cewar JIBWIS, wannan halin da Najeriya ta shiga ya kawo tsadar rayuwa da rashin kwanciyar hankali tsakanin yan ƙasa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Taron da ƙungiyar ta gudanar an masa take da: "Mahangar addinin musulunci kan taɓarɓarewar zaman lafiya da cigaba a Duniya."
KARANTA ANAN: Sakon Osinbajo ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, abubuwa za su daidaita
JIBWIS ta ƙara kira ga gwamnati da ta saka al'umma a cikin yaƙin da take da ta'addanci ta hanyar da ya dace.
Hakanan kuma ƙungiyar ta yi kira da a ƙirƙiri wani abu da fasahar zamani wanda zai taimaka wajen gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'addanci a ƙasar nan, kuma ya tabbatar an hukunta su dai-dai da abinda suka aikata.
A wani labarin kuma Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara
Shahararren malaminnan, Sheikh Gumi ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da safiyar yau don tattaunawa da shi.
Rahotanni sun tabbatar da zuwan malamin tare da wasu malaman addini kuma a yanzun haka suna tsakar tattaunawa da Obasanjo.
Asali: Legit.ng