'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi

'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi

- Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin Azir a karamar hukumar Damboa a Borno

- Sun halaka mutum guda daya sannan sun sace kayan abinci da dabobi da wasu kayayakin sannan sun kona gidaje

- Hakimin garin Damboa, Zanna Lawan Maina ya tabbatar da harin da aka kai a garin da ke hanyar Damboa zuwa Biu

Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne, a ranar Laraba sun kai hari garin Azir a karamar hukumar Damboa sun kashe mutum daya tare da raunata wasu da dama, rahoton Vanguard.

Yan ta'addan sun kuma sace kayan abinci da dabobi masu yawa bayan kone gidan mutanen garin.

'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi
'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

Wasu mazauna garin da ke hanyarsu na tserewa sun yi magana da wakilin majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce, "A halin yanzu mun fake a Damboa ba masauki babu abinci ga kuma sanyi na harmatan.

"Yan ta'addan sun afka garin mu sunyi ta'addi da kyar muka samu muka shiga daji kafin muka tsere zuwa Damboa."

Hakimin garin Damboa, Zanna Lawan Maina ya tabbatar da harin da aka kai wa mutanensa a hirar wayar tarho da ya yi da wakilin majiyar Legit.ng a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira

"Yan Boko Haram sun kai hari garin Azir, sun kashe mutum daya bayan sace kayan abinci, dabobi da wasu kayayyakin," a cewar hakimin na garin Damboa.

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Source: Legit

Online view pixel