Mutan Darmanawa na zargin Masarautar Kano da yunkurin sayar da Filin Idi

Mutan Darmanawa na zargin Masarautar Kano da yunkurin sayar da Filin Idi

- Matasan karamar hukumar Tarauni sun kai karar masarautar Kano wajen gwamnati

- Matasan sun zargi masarautar da yunkurin kwace filin Masallacin idin dake garin

- Sun bayyana cewa marigayi Sarki Ado Bayeroo ne ya bada filin don amfani

Wasu yan jihar Kano karkashin kungiyar cigaban Darmanawa Layout, na zargin asusun lamunin birnin Ado Bayero, wani asusun masarautar Kano, da yunkurin kwace filin Idi da kuma sayar da shi.

Shugaban kwamitin filin Idi, Barista Tijjani Yahaya, ya bayyanawa manema labarai a jihar Kano cewa marigayi Ado Bayero ne ya bayar da filin kyauta ga garin kuma gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan.

Tijjani Yahaya ya bayyana cewa irin haka ya taba faruwa a 2019 lokacin da wasu sukayi kokarin sayar da filin.

A cewarsa, Filin ita ce wajen Sallan idi daya tilo dake karamar hukumar Tarauni gaba daya.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa sun rubuta wasika ga hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa na jihar Kano a Oktoban 2020, domin hana masarautar kwace filin.

"Yayinda muke sauraron sakamakon wadannan kararraki da muka shigar, wakilan asusun lamunin birnin Ado Bayero sun yi kokarin kwace filin karfi da yaji kuma mun samu nasaran hanasu a 30 ga Disamban, 2020." Yace.

"Saboda haka, muna kira ga asusun lamunin Ado Bayero ta gabatar wani hujja dake nuna cewa filinta ne."

KU DUBA: Idan aka rage farashin mai, za'ayi wahalar mai kwanan nan, Ministan Mai

Mutan Darmanawa na zargin Masarautar Kano da yunkurin sayar da Filin Idi
Mutan Darmanawa na zargin Masarautar Kano da yunkurin sayar da Filin Idi Hoto: @dawisu
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar wahalar man fetur a fadin tarayya kwanan nan.

Yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago a ranar Litinin, 1 ga Febrairu, Timipre Sylva, karamin ministan mai, ya bayyana cewa da yiwuwan ayi wahalar mai idan yan kwadago suka zake kan cewa lallai sai an rage farashin mai, Channels TV ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng