Ba mu Amince da ƙarin wata ɗaya kacal ba - Wata Ƙungiya ta maida ma Pantami Martani

Ba mu Amince da ƙarin wata ɗaya kacal ba - Wata Ƙungiya ta maida ma Pantami Martani

- Da alama har yaanzin ministan Sadarwa Isa Pantami na kan bakarsa na rufe layukan waya waɗanda ba'a haɗa su da NIN ba

- Wata ƙungiyar masu anfani da kamfanonin sadarwa ta ce bata amince da karin wata ɗaya da gwamnati ta yi ba na haɗa layuka da NIN

- Ta ce yakamata gwamnatin ta nuna halin dattako ta yi biyayya ga umarnin da kotu ta bayar na kara watannin biyu

Wata ƙungiyar masu amfani da kamfanonin sadarwa tace bata amince da ƙarin wa'adin da gwamnatin tarayya ta yi ba kan haɗa layukan waya da lambar katin zama ɗan ƙasa (NIN).

Ƙungiyar tace yakamata gwamnati ta bi umarnin da kotu ta bayar na ƙara lokacin har tsawon wata biyu.

KARANTA ANAN: Ana binciken Aminu Ado Bayero da Mukarrabansa da badakalar Naira Biliyan 1.3

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa, ƙungiyar ta ce ƙarin wata ɗaya ya yi kaɗan kuma tana kira ga gwamnatin tarayya ta yi biyayya ga hukuncin da kotu ta yi ran 23 ga watan Maris.

A kwanakin baya dai wata babbar kotu dake zamanta a Lagos ta bada umarnin ƙara wa'adin rijistar NIN da tsawon wata biyu.

Mai shari'a M.A. Onyetenu ya bada umarnin ya yin da yake yanke hukunci kan ƙarar da lauyan dake fafutukar kare hakkin ɗan adam, Monday Ubani, ya shigar.

Lauyan ya shigar da ƙarar ne yana neman kotun da ta dakatar da ma'aikatar sadarwar kasar nan daga shirin ta na rufe layukan waya waɗanda ba'a haɗa su da NIN ba.

Da alama Pantami na kan bakarsa na rufe layukan waya, ya bayyana sabon Wa'adi kowa ya haɗa nashi da NIN
Da alama Pantami na kan bakarsa na rufe layukan waya, ya bayyana sabon Wa'adi kowa ya haɗa nashi da NIN Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Sai dai shugaban ƙungiyar masu amfani da kamfanonin sadarwa na ƙasar nan ya kira yi ma'aikatar sadarwar ƙasar nan da ta yi biyayya ga hukuncin kotu.

A cewar shugaban: "Bamu yarda da karin wata ɗaya ba, ya kamata ma'aikatar ta yi biyayya ga abinda kotu tace, ta ƙara wata biyu."

KARANTA ANAN: Shugaban kasan Japan ya nada 'ministan kadaici' bayan hauhawar kashe kai

Darakatan yaɗa labarai na hukumar kula da sadarwar ƙasar nan (NCC), Dr Ikechukwu Adinde, ya bayyana matsayar gwamnati na ƙara wa'adin wata ɗaya.

Ya ce an amince da ƙarin ne a wani taro da aka gudanar ran Alhamis tare da masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa wanda ministan sadarwa Isa Pantami ya jagoranta.

Ya kuma ƙara da cewa shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan ƙarin na wata ɗaya.

A wani labarin kuma Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

Kasar Amurka ta zargi gwamatin Najeriya da yin shuru kan lamarin kisan almajiran Zakzaky.

Amurka ta ce ya kamata ya zuwa yanzu Najeriya ta ito ta fadawa duniya halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel