Batan jirgin yaki: NAF ta yi martani kan bidiyon da Boko Haram ta saki

Batan jirgin yaki: NAF ta yi martani kan bidiyon da Boko Haram ta saki

- Sojojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin ƴan ƙungiyar Boko Haram na harbo jirgin yaƙin sojin tun daga sama

- Dama jirgin yaƙin ya tafka hatsari kuma ya ɓata ne tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris, kamar yadda aka tabbatar

- Saidai ƴan boko Haram sun yi bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka tafka wannan aika-aikar

Sojojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin da ƴan ƙungiyar boko haram suka yi a wani bidiyo na harbo jirgin yaƙin sojojin da aka nema aka rasa tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Boko haram sun saki wani bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka harbo jirgin yaƙin.

Sa idai babban jami'in hulɗa da jama'a na sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya musanta maganar wannan bidiyon da ƴan Boko Haram suka saki.

KU KARANTA: Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya

Batan jirgin yaki: NAF ta yi martani kan bidiyon da Boko Haram ta saki
Batan jirgin yaki: NAF ta yi martani kan bidiyon da Boko Haram ta saki. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gidan yari, Pantami

Ya ƙara da tabbatar wa da duniya cewa ƴan Boko Haram sun lailayo wata ƙaryar ne kawai suka maka duk don su ƙara wa labarin armashi amma maganar gaskiya ba haka bane.

Kamar yadda kakakin NAF din, Air Commodore Edward Gibkwet yace: "Mun ga wasu bidiyoyi suna yawo wadanda babu wata alama da take nuna cewa jirgin namu ne, ko kuma wani matuƙin jirginmu ko kuma alamar jirginmu ne wannan wanda suke nunawa.

"Da alama wani bidiyo ne can daban da aka ɗauka a wani wuri wanda ko shuke-shuken wurin ba na arewa maso yamma bane. Suna ta sakin bidiyoyin da kadan-kadan kuma muna kallo."

A wani labari na daban, Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.

Jaridar The Cable ta bayyana yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.

Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng