Da duminsa: Mu muka baro jirgin yakin Najeriya: Yan ta'addan Boko Haram sun saki bidiyon jirgin
- Bayan kwanaki biyu da bacewar jirgin Soji, yan Boko Haram sun saki bidiyo
- Bidiyon ya nuna gawar daya daga cikin Sojojin dake tukin jirgin
- Hukumar Soji ba tayi tsokaci kan wannan ikirari na Boko Haram ba har yanzu
Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram, bangaren Abubakar Shekau, sun dauki alhakin baro jirgin yakin hukumar Sojojin Najeriya Alpha Jet NAF475.
Zaku tuna cewa a ranar Laraba hukumar sojin sama ta bayyana cewa jirginta ya bace a sararin samaniya a jihar Borno.
An tura jirgin taimakawa Sojojin kasa dake yakin yan Boko Haram.
Da safiyar Juma'a, hukumar Sojin saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa jirgin yakinta Alpha Jet (NAF475) da ta bace a sararin samaniya ta yi hadari.
Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Da yammacin Juma'a kuwa, yan ta'addan Boko Haram suka saki bidiyo inda yake ikirarin su suka baro jirgin
A cewar HumAngle, bidiyon da Boko Haram ta saki ya nuna mambobin kungiyar rike da rokoki da kuma gawar daya daga cikin matukan jirgin da suka baro.
KU KARANTA: An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar
DUBA NAN: Akwai yan bindiga 30,000 a Arewacin Najeriya, Gwamnan Zamfara Matawalle
A ranar 21 ga Febrairu, hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da labarin hadarin jirginga inda ta sanar da adadin mutanen da suka mutu a hadari.
Kakakin hukumar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkan mutane bakwai dake cikin jirgin ne suka rasa rayukansu.
Ya kara da cewa Sojojin sun tafi neman daliban Kagara da yan bindiga suka sace ne.
Asali: Legit.ng