Akwai yan bindiga 30,000 a Arewacin Najeriya, Gwamnan Zamfara Matawalle
- Jihar Zamfara na cikin jihohin Arewa maso yamma da yan binbida suka addaba shekarun nan
- Makonni bayan shiga sabon shekara, yan bindiga sun kwashe kimanin dalibai 300 a makarantar kwana
- Gwamnan jihar ya ce zai cigaba da sulhu da yan bindigan saboda hakan ya fi
Gwamnan jihar Zamfara, Mohammad Bello Matawalle, ya bayyana cewa akwai kimanin yan bindiga 30,000 a jiharsa da kuma wasu jihohin Arewacin Najeriya biyar.
A cewar gwamnan, akwai akalla sansanonin tsagerun yan bindiga 100 kuma kowace sansani na da akalla yan bindiga 300.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin sabon kwamishanan labaransa, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, a hira da manema labarai ranar Juma'a a jihar Kaduna, rahoton Daily Trust.
Sauran jihohin Arewan da ya ambata sune Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna da Niger.
Ya ce gwamnatin tarayya ba ta da isasshen jami'an da zasu iya yaki da wadannan tsagerun yan bindigan ba.
Ya ce gaba daya Sojojin dake yankin Arewa maso yamma basu wuce 6000.
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya koma kudu a 2023
DUBA NAN: An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar
A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya jaddada matsayarsa na cewa Najeriya ta fi karfi tare da tsayuwa a matsayinta na kasa daya.
Don haka yayi kira ga 'yan kasa da kada su bar masu bata musu suna su raba kasar nan.
Matsayar Buhari na kunshe ne a sakon ista wanda shugaban kasan ya taya 'yan Najeriya mabiya addinin Kirista murnar bikin, wanda Femi Adesina ya mika ga manema labarai.
Asali: Legit.ng