An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar

An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar

- A bikin mai armashi, sabon shugaban jamhurriyar Nijar ya sha rantsuwa

- Wannan shine karo na farko da gwamnatin demokradiyya za ta mika mulki ga zababben shugaba

- Taron ranstsarwan ya samu halartan manyan masu fada aji daga Najeriya

Kwanaki biyu bayan Sojoji sukayi yunkurin juyin mulki, an rantsar da Mohamed Bazoum, a matsayin sabon shugaban kasar jamhuriyyar Nijar.

An rantsar da shi ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Afrilu, 2021.

Gabanin yanzu, Bazoum ya kasance Ministan harkokin cikin gida kuma babban na hannun daman shugaba mai barin gado, Mahamadou Issoufou.

Wannan shine karo na farko tun lokacin da janhurriyar Nija ta samu yanci daga mulkin mallakar kasar Faransa da wani shugaban demokradiyya zai mika mulki ga wani shugaba ta hanyar zabe.

Sau hudu ana juyin mulki a tarihin kasar Nijar, mafi kusa wanda ya faru Febrairun 2010 inda aka tunbuke shugaba a lokacin, Mamadou Tandja.

Amma cikin awanni 48 da suka gabata, kasar ta fuskanci barazana da dama daga wasu yan yunkurin tada zaune tsaye.

Daga cikin wadanda suka halarci taron rantsar da Bazoum akwai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Attajiri Alhaji Aliko Dangote, da Sarkin Kano mai murabus, Muhammadu Sanusi II.

KU KARANTA: Akwai yan bindiga 30,000 a Arewacin Najeriya, Gwamnan Zamfara Matawalle

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya zoma kudu a 2023

An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar
An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar
Source: Twitter

A safiyar Laraba, 31 ga watan Maris ne aka wayi gari da fargabar a kasar inda aka dauki tsawon lokaci ana harbe-harben bindiga a babban birnin Yamai.

Mazauna birnin sun ce, sun kwashe tsawon dare suna jiyo karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasar.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta ce, tuni aka damke sojojin da ake zargi da kulla-kullan juyin mulkin da bai yi nasara ba, kafar labarai ta RFI ta ruwaito.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel