Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya yi hadari a Abuja, dukkan wadanda ke ciki sun mutu, NAF

Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya yi hadari a Abuja, dukkan wadanda ke ciki sun mutu, NAF

- Jirgin Sojojin sama ya yi hadari yana gab da sauka a tashar jirgin Abuja

- Dukkan wadanda ke cikin jirgin sun rasa rayukansu

- Masu Idanuwan shaida sun bayyana cewa jirgin ya kone kurmus

Labarin da ke shigo mana da duminsa na cewa wani jirgin sama ya yi hadari a birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, 21 ga Febrairu, 2021.

Ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika, ya tabbatar da labarin a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita.

Hadi Sirika ya ce jirgin na Sojoji ne wanda ya fada bayan yan dakikai da tashi sama daga tashar jirgin saman Abuja.

Yace: "Wani jirgin saman Soji King Air 350 ya yi hadari a tashar jirgin sama bayan samun matsalan inji a hanyar zuwa Minna. Da alamun abin ya yi muni."

Hakazalika hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da labarin inda ta sanar da adadin mutanen da suka mutu a hadari.

Kakakin hukumar, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkan mutane bakwai dake cikin jirgin ne suka rasa rayukansu.

Yace: "Muna tabbatar da labarin cewa jirgin hukumar mayakan sama, Beechcraft KingAir B350i ya fadi yayin dawowa Abuja daga Minna sakamakon matsalar inji."

"Dukkan mutane 7 dake cikin jirgin suka mutu."

KU KARANTA: 2023: Jerin manyan arewa dake goyon bayan mayar da mulkin Najeriya Kudu

KU DUBA: Ba kudin fansa 'yan bindiga suke nema ba kafin su sako daliban Kagara, in ji Sheikh Gumi

A bangare guda, kwamitin kwararru na kula da COVID-19 na jihar Kano, ya bullo da wani shiri na kula dada gida don kai wa ga mutane a yankuna masu nisa, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.

Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar wanda jami’in yada labaran ta Mista Maikudi Marafa ya sanya hannu, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel