'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun

'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun

- 'Yan bindiga masu tarin yawa sun kutsa sansanin jami'an tsaro a Niger inda suka kashe wasu sojoji

- An gano cewa miyagun sun kai hare-hare a ranakun Laraba da na Alhamis karamar hukumar Shiroro

- Miyagun da za su kai 100 sun kutsa kauyukan Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki inda suka ci karensu babu babbaka

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe sojoji a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

An gano cewa 'yan bindigan sun sace sama da mutum 10, sun sace babura bakwai tare da kone ababen hawan sojoji a wasu hari da suka kai ranar Laraba da sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yankunan da 'yan bindigan suka kai hari sun hada da Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki duk a karamar hukumar Shiroro.

KU KARANTA: Duk da kiran allurar riga-kafin korona da 'mugunta', Fani-Kayode ya je an yi mishi

'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun
'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'

An gano cewa 'yan bindigan sun shiga sansanin jami'an tsaron hadin guiwa da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan sa kai a Allawa kuma suka bude musu wuta.

An kashe jami'in NSCDC a take yayin da wasu jami'an tsaron suka samu miyagun raunika.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Manta, Gurmana da Bassa a ranar Laraba, inda suka kashe wani Alhaji Sale dake yankin Madalla kuma suka sace mutum 4.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban kungiyar matasan Shiroro, Mohammed Sani Idris, ya ce 'yan bindigan da suka kai 100 ne suka shiga yankin da AK47.

Sun yi barna a yankin na tsawon sa'o;i biyar ba tare da an yi musu martani ba.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce jami'an tsaro sun damke wasu 'yan Najeriya dake daukar nauyin ta'addancin Boko Haram.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.

Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama'a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: