'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gidan yari, Pantami

'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gidan yari, Pantami

- Akwai yuwuwar gwamnatin Najeriya ta ɗaure duk 'yan Najeriyan da ba su yi rijistar 'yan ƙasa ba a gidan gyaran hali

- Ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami ya sanar da manema labaran cikin gidan gwamnati a Abuja cewa babu mara rijistar da zai sake morar romon damokradiyya

- A cewarsa, gwamnati za ta tabbatar da wannan hukuncin bisa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma zata tilasta yin rijistar akan kowa

Za a ɗaure ƴan Najeriyan da suka ƙi yin rijistar ƴan ƙasa a gidan gyaran hali, don babu wanda zai mori romon damokradiyya ba tare da rijista ba a cewar ministan sadarwa, Dr Isa Pantami.

Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Pantami ya bayyana hakan a wani taro da suka yi na ministoci a gidan gwamnati dake Abuja.

Ya bayyana yadda aka yanke shawarar ta ɗaure marasa rijistar inda yace hakan ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasar nan don kada wani mara rijista ya mori romon demokraɗiiyya.

KU KARANTA: Duk da kiran allurar riga-kafin korona da 'mugunta', Fani-Kayode ya je an yi mishi

'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gida yari, Pantami
'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gida yari, Pantami. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

Pantami ya nuna muhimmancin samun lambar rijistar don sadata da layukan wayar mutum da kuma sauran ayyuka da yanzu aka wajabta dole sai an haɗa da ita lambar katin.

A cewar Pantami, baya ga ƙidayar yawan ƴan ƙasa, yin rijistar zai samar da yawan adadin ƴan Najeriya saboda tsananin muhimmanci.

A cewar ministan fiye da ƴan Najeriya 51,000,000 ne suka riga suka yi rijistar kuma wajibi ne yin hakan.

A wani labari na daban, Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya yi allurar riga-kafin cutar korona ta AstraZeneca.

A watan Afirilun 2020, tsohon ministan ya kwatanta riga-kafin cutar corona da muguntar da za ta yi sakamakon mutuwar mililoyin jama'a.

A watan Mayun 2020, yayin da ake ta cigaba da samar da riga-kafin cutar, tsohon ministan sufurin jiragen saman ya kushe wannan cigaba a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa an mayar da mutane "aladun turawa".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng