Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga

Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga

- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Charles Soludo, ya ce an yi musayar wuta tsakanin ƴan bindiga da ƴan sanda na tsawon mintina 15 da suka kai mishi hari

- Kamar yadda labarai suka bayyana, ƴan bindiga sun kai wa Soludo hari ne a ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba

- A harin ƴan sanda 3 ne suka rasa rayukansu sannan kuma ƴan bindigan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne

Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.

Jaridar The Cable ta bayyana yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.

Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.

KU KARANTA: Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga
Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

A wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan talabijin ɗin Channels, tsohon gwamnan bankin ya bayyana yadda ya fara jin harbe-harbe yayin da ya kusa kammala bayani a taron.

Tsohon gwamnan bankin yace ya zaci ƴan sanda ne suke harbi a iska a lokacin da aka fara musayar wutar. Ya ƙara da bayyana yadda kowa ya tsere don neman tsira.

A cewarsa sai daga baya suka ga gawar ƴan sandan yayin da jini yayi face-face a wurin.

"Ina cikin shirye-shiryen kammala bayanai sai naji harbe-harben bindigogi. Na zaci ƴan sanda ne ashe ƴan bindiga ne," a cewarsa.

"Sai da naji mutane suna ihu suna guje-guje don neman tsira. Sai da aka yi mintuna akalla 15 ana fafatawa da harbe-harbe suka tsaya.

"A lokacin da muka dawo sai muka ga gawar ƴan sanda uku a ƙasa cikin jini. Muna musu fatan rahamar Ubangiji," cewar Soludo.

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe sojoji a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

An gano cewa 'yan bindigan sun sace sama da mutum 10, sun sace babura bakwai tare da kone ababen hawan sojoji a wasu hari da suka kai ranar Laraba da sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yankunan da 'yan bindigan suka kai hari sun hada da Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki duk a karamar hukumar Shiroro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: