Kotu ta yankewa madamfari hukuncin shekaru 70 a gidan yari

Kotu ta yankewa madamfari hukuncin shekaru 70 a gidan yari

- Bayan shekaru biyu ana shari'a, kotu ta yanke hukunci kan dan damfara a Sokoto

- Mutumin ya damfari wasu mata da ya yiwa alkawarin ninka musu kudi a kasuwancin gwal

- Kotu ta yanke masa shekaru bakwai-bakwai har sau 10 kan dukkan laifukan

Babban kotun jihar Sokoto a ranar Alhamis ta yankewa wani mai damfara, Hamzat Muhammad Bashar, hukuncin shekaru 70 a gidan yari kan laifin damfarar mutane kimanin milyan 30.

Hukumar EFCC ta shigar da Hamzat kotu tun ranar 7 ga Nuwamba, 2019 kan zargin laifuka 12 da suka hada da damfara, yaudara, da zamba cikin aminci.

EFCC ta ce mutumin tare da wata mata Hindatu Bashir sun karbi kudi milyan N23,760,000 hannun Hadiza Aliyu da sunan sanya hannun jari cikin kasuwancin zinari amma ba zata sake ji daga garesu ba.

A jawabin da EFCC ta saki, ta ce lauyanta Habila Jonathan, ya gabatar da shaidu 10 da hujjoji kan tabbatar da laifin da ake zargin mutumin da shi.

Lauyan ya bayyanawa kotu cewa Hamza da abokiyar aikinsa sun aikata wannan laifi a shekarar 2018.

Yayinda da Alkali kotun, Duwale, ya yanke hukumar yau, ya kama Hamza da laifuka goma cikin 12 da aka zarginsa da su kuma ya yanke masa shekaru bakwai kan kowani laifi.

Bugu da kari, Alkalin ya umurci madamfarin ya mayar da kudi milyan N29, 135,000 ga wadanda ya damfara ta hannun EFCC, hukumar ta bayyana.

DUBA NAN: Gwamnati Ba Za Ta Manta Da Gajiyayyu Da Talakawa Ba, Buhari Ya Tabbatarwa 'Yan Nigeria

Kotu ta yankewa madamfari hukuncin shekaru 70 a gidan yari
Kotu ta yankewa madamfari hukuncin shekaru 70 a gidan yari Credit: EFCC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran Hanyar Abuja Zuwa Kano

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya jaddada matsayarsa na cewa Najeriya ta fi karfi tare da tsayuwa a matsayinta na kasa daya.

A don haka yayi kira ga 'yan kasa da kada su bar masu bata musu suna su raba kasar nan.

Matsayar Buhari na kunshe ne a sakon ista wanda shugaban kasan ya taya 'yan Najeriya mabiya addinin Kirista murnar bikin, wanda Femi Adesina ya mika ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel