Batan Jirgin Yaƙi: Shugaban Rundunar Sojojin Sama ya Dira Maiduguri

Batan Jirgin Yaƙi: Shugaban Rundunar Sojojin Sama ya Dira Maiduguri

- Shugaban rundunar sojin saman ƙasar nan (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya dira Borno don ƙarfafa binciken nemo jirgin yaƙin sama da ya ɓata

- Da isar CAS ɗin ya tattauna jami'ansa da matuƙa jirgin saman rundunar ya roƙe su da su maida hankali sosai kan binciken

- An sanar da batan jirgin yakin a jiya Laraba 31 ga watan Maris, inda aka bayyana cewa jirgin ya ɓata ne ya yin taimakawa sojojin ƙasa

Shugaban rundunar sojin sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya yin da ake cigaba da neman jirgin da ya ɓata ya ƙara tsananta.

KARANTA ANAN: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Daraktan yaɗa labari na rundunar, Edward Gabkwet, ya bayyana cewa bayan isar shugaban an yi masa bayani kan ƙoƙarin da ake yi na gano jirgin da ga ɓata.

A wani taro da suka gudanar bayan isar sa tare da jami'an tsaro, Amao ya roƙi matuƙa jirgin sama da injiniyoyi da su mai hankali sosai kan aikin su don tabbatar da zaman lafiya ya dawo yankin Arewa maso gabashin ƙasar nan.

Har yanzun babu wata shaida ƙwakƙwara dake nuna cewa ko mayaƙan Boko Haram ne suka kakkaɓo jirgin.

Batan Jirgin Yaƙi: Shugaban Rundunar Sojojin Sama ya Dira Maiduguri
Batan Jirgin Yaƙi: Shugaban Rundunar Sojojin Sama ya Dira Maiduguri Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Ko kuma mayaƙan ISWAP ne suka harbo jirgin ko kuwa matsala jirgin ya samu ya yi hatsari a wani wuri.

Da farko dai Daraktan yaɗa labarai na sojin sama, Gabkwet ne ya fara sanar wa yan Najeriya ɓatan jirgin a jiya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira

Yace jirgin na cikin aikinsa na taimakawa wa sojoji a yankin arewa maso gabas, kwatsam sai aka rasa sadarwar jirgin.

Daga baya aka gano jirgin na aiki ne a jihar Borno, a yakin da ake da mayaƙan Boko Haram da na ISWAF.

Ya ce an rass duk wata sadarws ts jirgin ya yin da yake tsakiyar aikin taimakawa sojojin ƙasa, amma ana cigaba da ƙoƙarin gano ina yake a yanzu.

A jawabin da aka fitar ya nuna jirgin ya ɓata ne da misalin ƙarfe 5:08 na yammacin Laraba, 31 ga watan Maris.

A wani labarin kuma Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Har yanzu yan bindiga sun ki sakin malamin nan na Kano Sheikh Abdullahi Shehu Mai Annabi bayan biyan kudin fansa.

Maimakon haka ma, maharan sun saki gawarwakin mutum hudu cikin wadanda aka sace tare da Mai Annabi.

Source: Legit

Online view pixel