'Yan Najeriya na ƙaunar Jam'iyyar mu ta APC, Yakamata a ƙara lokacin yin Rijista - Shuwagabannin APC na jihohi

'Yan Najeriya na ƙaunar Jam'iyyar mu ta APC, Yakamata a ƙara lokacin yin Rijista - Shuwagabannin APC na jihohi

- Ƙungiyar shuwagabannin APC na jihohin ƙasar nan sun yi kira ga uwar jam'iyya ta ƙasa da ta ƙasa wa'adin yin rijistar zama cikakken ɗan APC

- Shugaban ƙungiyar, wanda shine shugaban APC reshen jihar Borno ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga wani taro a Abuja

- Ya ce al'ummar Najeriya na ƙaunar jam'iyyar shiyasa ma suka fito ƙwansu da ƙwarƙwata don yin rijistar zama ɗan APC

Ƙungiyar shuwagabannin jam'iyyar APC na jihohi sun yi kira ga uwar jam'iyyar ta ƙasa da ta ƙara lokacin yin rijista dan zama ɗan jam'iyya.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Likitocin ƙasar nan sun tsunduma yajin Aiki

Shugabannin sun yi wannn kira ne a wani taron manema labarai da suka kira ranar Alhamis jim kaɗan bayan fitowa daga wani taron sirri a Abuja.

Shugaban ƙungiyar, Ali Buka-Dalori, ya yi ƙarin haske da cewa ƙarin lokacin ya zama wajibi domin baiwa yan Najeriya dama su shigo jam'iyyar.

Ya bayyana cewa dandazon mutanen dake fitowa dan yin rijistar da kuma ƙarfin da jam'iyyar ke ƙara yi a yan watannin nan ya nuna cewa akwai sauran mutane da dama dake son shiga jam'iyyar ta APC nan gaba.

'Yan Najeriya na ƙaunar Jam'iyyar mu ta APC, Yakamata a ƙara lokacin yin Rijista - Shuwagabannin APC na jihohi
'Yan Najeriya na ƙaunar Jam'iyyar mu ta APC, Yakamata a ƙara lokacin yin Rijista - Shuwagabannin APC na jihohi Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

A bayaninsa yace:

"Mu shuwagabannin jihohi muna kira ga shuwagabannin APC na ƙasa da su duba bukatar jam'iyyar da kuma mambobinta na faɗin ƙasar nan su ƙara lokacin gudanar da rijista domin zama cikakken ɗan jam'iyya."

KARANTA ANAN: Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Ya ce suna buƙatar ƙarin lokaci domin kawo ma jam'iyyar yan Najeriya da suke son yin rijista, kamar yadda channels TV ta ruwaito.

Ali Buka-Dalori, wanda shine shugaban APC na jihar Borno ya koka kan yadda jam'iyyar ke tafiyar da rabon kayan rijista ɗin.

Wanda haka yasa wasu jihohin ƙasar nan basu daɗe da samun kayayyakin da zasu cigaba da yin rijistar zama ɗan APC a karo na biyu da wuri ba.

Shugaban ƙungiyar ya kuma jinjina ma uwar jam'iƴyar APC ta ƙasa kan ƙirƙiro da yin rijistar, yana mai bayyana hakan a cigaban da ake maraba da shi.

A wani labarin kuma NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Hukumar Kula Da Igancin Magunguna da Abinci, NAFDAC, ta gano abinda yayi sanadin bullar bakuwar cuta a Kano.

NAFDAC ta ce gwajin da ta yi ya nuna cewa wani sanidarin mai guba ne da ake sayar da shi da suna 'citric acid' ko 'Dan Sanmi'.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel