Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Likitocin ƙasar nan sun tsunduma yajin Aiki
- Ƙungiyar likitocin cikin gida NARD ta bayyana shiga yajin aiki tun daga yau ɗaya ga watan Afrilun wannan shekara 2021
- Duk da ƙoƙarin da ministan ƙwadigo na ƙasar nan, Chris Ngige ya yi na warware matsalolin su jiya amma abun ya ci tura
- NARD ta bayyana a shafin ta na kafar sada zumunta tuwita cewa bata yanke wannan hukuncin na shiga yajin aiki don ta cutar da yan Najeriya ba
Ƙungiyar likitocin ƙasar nan NARD sun tsunduma yajin aiki daga yau ɗaya ga watan Afrilu 2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: ‘Yan fashi sun yi wa ‘Yan Sanda shelar zuwa, kuma sun fasa bankuna da rana sun saci miliyoyi
Ƙungiyar ta bayyana fara yajin aikin ne da safiyar yau Alhamis duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya tayi na dakatar da hakan a daren jiya.
Likitocin sun tabbatar wa yan Najeriya da cewa ba su yanke shiga yajin aikin bane don su cutar da kowa.
NARD ta bayyana haka ne a wani bayani da tayi a shafinta na kafar sada zumunta wato tuwita da safiyar yau Alhamis.
Kungiyar ta yi bayani kamar haka:
"Yakamata yan Najeriya su gane cewa muna ƙaunar su kuma wannan yajin aikin ba yana nufin mu cutar da su bane, sai dan mu ƙalubalanci gwamnatin tarayya waɗanda ɗaya daga cikin haƙƙoƙin dake kanta shine ta kula da yan ƙasar ta da kuma ma'aikatanta wajen yin duk abinda ya kamata."
KARANTA ANAN: Pantami, kamfanonin sadarwa zasu yi taro kan hukuncin kotu na dakatar da rufe layukan waya
Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, ya tabbatar da sun shiga yajin aiki tun daga ƙarfe takwas na safiyar yau Alhamis.
Yajin aikin likitocin yazo dai-dai lokacin da shugaban ƙasa mejo janar Muhammadu Buhari ya tafi Landan domin duba lafiyarsa.
A wani labarin Kuma Barayi sun afka gidan jarumin Kannywood, sun yi awon gaba da sabuwar motarsa da wasu muhimman kayayyaki
Wasu barayi dauke da muggan makamai sun shiga gidan wani fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Nasiru Bello Sani, wanda aka fi sani da Nasiru Naba da misalin karfe 1:00 zuwa 2:00 na safiyar Laraba.
Sun kuma yi awon gaba da sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja.
Asali: Legit.ng