Matashi ya kashe matarsa kan Kunun karin kumallo a jihar Neja

Matashi ya kashe matarsa kan Kunun karin kumallo a jihar Neja

- An damke mutumin da ya kashe matarsa da duka a jihar Neja

- Wannan ya biyo bayan labarin wacce ta kashe kishiyarta a Nijar

- Hukumar yan sanda ta sanar da lokacin da zai gurfanar a kotu

Wani matashi dan shekara 20 ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar Neja kan laifin kisan matarsa kan sabanin da suka samu kan Kunun karin kumallon da tayi masa.

Bayan sabanin da suka samu, Danladiya bugi matarsa, Zulai Lawal, har ta sume. Daga baya ta mutu a asibiti, rahoton TheNation.

Yayinda aka bayyanashi a hedkwatar hukumar yan sandan jihar dake Minna, Danladi ya bayyana cewa bai taba tunanin matarsa za ta mutu sakamakon bugun ba.

Ya ce sun shiga dagawa juna murya ne lokacin da ya nuna rashin jin dadin kunun da tayi masa, kuma daga nan ya shiga bugunta.

"Ban taba tunanin za ta mutu ba. Kawai sabani muka samu kan Kunu kuma ban san lokacin da ta sume ba zata tashi ba. Da na sani ban bugeta ba, ina nadama," yace.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an damke Danladi ne a kauyen Kadaura dake karamar hukumar Rafi.

Abiodun ya ce an kaddamar da bincike kan lamarin kuma za'a gurfanar da shi a kotu.

KU DUBA: Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhurriyar Nijar

Matashi ya kashe matarsa kan Kunun karin kumallo a jihar Neja
Matashi ya kashe matarsa kan Kunun karin kumallo a jihar Neja
Asali: Twitter

A wani labarin kuwa, daya daga ciki yan ƙungiyar shi'a (IMN) ya mutu a ya yin da jami'an yan sandan Abuja ke ƙoƙarin tarwatsa gungun mambobin ƙungiyar dake zanga-zanga a babban birnin tarayya.

KARANTA ANAN: Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

Sai dai har yanzin rundunar yan sandan birnin tarayya, Abuja, basu ce komai game da lamarin ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Duk da cewa rahoton ya bayyana cewa wani harsashi ne da ba shi aka nufa dashi ba ya kashe shi kuma wasu da yawa sun jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel