Gwamna Ortom ya sha alwashin zaƙulo duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi ma Limamin Cocin Katolika

Gwamna Ortom ya sha alwashin zaƙulo duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi ma Limamin Cocin Katolika

- Gwamna Samuel Ortom ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa zata kamo duk wanda ke da hannu a kisan malamin cocin katolika

- Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne ta bakin sakataren yaɗa labaran sa a ranar Laraba

- Ya kuma yi kira ga al'umnar jihar da su kwantar da hankalinsu kuma su cigaba da baiwa jam'an tsaro goyon baya da sanar dasu duk wani abu da suke zargi don ɗaukar mataki

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya tabbatar da cewa duk wanda ke da hannu a kisan da akayi ma fadan cocin katolika, Fr. Ferdinand Ngugban, za'a kamoshi a hukunta shi.

KARANTA ANAN: Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista

Gwamnan ya yi wannan alƙawari ne a wani jawabi da sakataren yaɗa labaran sa, Mr Terver Akase, ya fitar a Makurɗi ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.

Ngugban, wanda shine limamin cocin katolika a kauyen Aye-Twar ƙaramar hukumar Katsina-Ala, an kashe shi ran Talata a cikin harabar cocin.

Gwamna Ortom ya yi Allah wadai da kisan, ya kuma tabbatar da gwamnatinsa zata yi duk me yuwu wa ta kamo waɗanda suka aikata kisan ta gurfanar dasu a gaban kotu.

"Ina tabbatar ma mutanen Katsina-Ala cewa gwamnatin jihar mu ba zata rintsa ba har sai ta kamo waɗanda ke da hannu a kisan da sauran hare-haren da aka kai yankin don a gurafanar da su a gaban ƙuliya." inji gwamnan.

Gwamna Ortom ya sha alwashin zaƙulo duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi ma Limamin Cocin Katolika
Gwamna Ortom ya sha alwashin zaƙulo duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi ma Limamin Cocin Katolika Hoto: @GovSamuelOrtom
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Gwamnatin Najeriya ta na neman haramta kawo motar da ta shekara 7 a Duniya

Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin "wanda bai kamata ba" kuma yana mamakin ko meyasa yan bindiga ke harin mutanen kirki irin fada.

Ya kuma ƙara jaddada cewa gwamnatinsa baza ta miƙa jihar ga yan ta'adda ba, ya kuma roƙi mutanen dake jihar Benuwe da su cigaba da taimakawa jami'an tsaron jihar da masaniya idan bukatar haka ta taso.

Daga ƙarshe gwamna Samuel Orton ya yi jaje ga iyalan malamin cocin tare da addu'ar Allah ya jikansa.

A wani labarin kuma Takarar Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga gwamnonin arewa da masu ruwa da tsaki

Shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na iya samun tikitin jam’iyyar gabanin takarar shugaban kasa a 2023.

Akwai alamu da ke nuna cewa tsohon gwamnan na jihar ta Legas na samun goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: