Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira

Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira

- 'Yan sandan jihar Akwa Ibom sun damke matar aure da ta yi wa dan kishiya duka har ya mutu

- Christiana wilson ta gayyaci wasu mutum uku inda suka kai dan mijinta bayan gari suka zane shi har ya mutu sannan suka birne shi

- Bayan kwanaki shida da aukuwar lamarin, Christiana ta je ta hako shi tare da cire masa kai ta birne a wani wuri saboda fatalwarsa na damunta

Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta cafke wata mata da ake zargi da hada kai da wasu mutum uku suka sace dan kishiyarta sannan suka lakada masa mugun duka har ya mutu.

Matar mai suna Christiana Wilson ta tabbatar da cewa ita da wasu mutum uku ne suka sace Edidiong Wilson mai shekaru 19 kuma suka kaishi daji tare da yi masa dukan kisa.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, bayan mutuwarsa, sun birne gawarsa a ranar 24 ga watan Disamban 2020, kamar yadda takardar 'yan sandan ta nuna a ranar 26 ga watan Maris.

Ana zargin sun aikata laifin ne a Ikot Usekong dake karamar hukumar Eket ta jihar Akwa Ibom.

Sauran wadanda ake zargi da laifin sun hada da Saviour Peter, Richard Ekpenyong da Dominic Usoro.

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin soji, mutum 9 sun sheka lahira a Dabanga

Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira
Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gagarumar gobara ta lashe kasuwar doya ta Namu dake Filato

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, ya ce Wilson ta koma inda suka birne yaron bayan kwana shida inda ta hako gawarsa tare da cire kansa ta birne a wuri daban, inda tayi ikirarin cewa fatalwar yaron tana damunta.

Kamar yadda Wilson ta sanar da 'yan sanda, ta dauka wannan matakin kan yaron ne saboda ya batar mata da wata N100,000 da ta bashi ajiya.

A wani labari na daban, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan karfafa yaki da rashawa da yayi a jihar.

Tinubu ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da gyararrun ofisoshin hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Idan za mu tuna, Tinubu ya isa jihar Kano ne wurin taron kwararru karo na 12, taron da ya shirya domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel