Boko Haram da 'yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya

Boko Haram da 'yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya

- Ministan tsaron kasa, Bashir Magashi, ya ce Najeriya tana fuskantar zaman lafiya

- Ministan ya sanar da hakan ne yayin ziyarar da kwamitin tsaro na majalisar tarayya ya kai masa

- Magashi yace da tallafin majalisar dattawa tare da na ma'aikatarsa, kalubalen tsaron kasar nan zai zama tarihi

Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce kasar nan na fuskantar zaman lafiya duk da irin kalubelen tsaro da take ciki.

Rundunar sojin kasar nan sun kasance suna yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sama da shekaru 10.

The Cable ta ruwaito cewa, dakarun suna cigaba da gwagwarmaya da 'yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno

Rashin tsaro: Mun samar da kwanciyar hankali a Najeriya, Ministan tsaro
Rashin tsaro: Mun samar da kwanciyar hankali a Najeriya, Ministan tsaro. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A yayin karbar kwamitin majalisar dattawa a kan lamarin tsaro a ranar Talata, ya ce an kashe jami'an tsaro a wasu wurare amma duk da haka rundunar sojin kasar nan ta samu nasara.

"Najeriya tana fama da matsalar tsaron cikin gida sakamakon addabar da mayakan Boko Haram suka yi a arewa maso gabas da kuma 'yan bindiga a jihohin Niger, Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara," yace.

“Wadannan kalubalen sun matuukar zama dalilan da suka sa muke rasa zakakuran dakarunmu dake kan aiki."

Magashi yace da taimakon majalisar dattawa, ma'aikatarsa za ta cigaba da aikin da ya dace tare da samun zaman lafiyan da Najeriya ke bukata.

A bangarensa, Aliyu Wamakko, wanda ya jagoranci kwamitin majalisar, ya ce yana da tabbacin Najeriya za ta shawo kan matsalolin tsaro da suke ci mata tuwo a kwarya.

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin soji, mutum 9 sun sheka lahira a Dabanga

A wani labari na daban, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan karfafa yaki da rashawa da yayi a jihar.

Tinubu ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da gyararrun ofisoshin hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Idan za mu tuna, Tinubu ya isa jihar Kano ne wurin taron kwararru karo na 12, taron da ya shirya domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel