Gwamnatin Najeriya ta na neman haramta kawo motar da ta shekara 7 a Duniya

Gwamnatin Najeriya ta na neman haramta kawo motar da ta shekara 7 a Duniya

- Kwastam ta kawo shawarar a daina shigo da motocin da su ka yi rugu-rugu

- Shugaban Hukumar ya na so a hana shigo da motar da aka hau na shekara 7

- Hameed Ali ya ce kudin da jami’an hukumar kwastam su ke samu ya ragu

Majalisar wakilan tarayya ta bukaci a kara yawan kudin da hukumar kwastam ta ke harin za ta samu a shekarar nan, Punch ta fitar da wannan rahoto.

Kwamitin kwastam a majalisar wakilai ta tashi da kudin da hukumar ke burin tattaro wa a shekarar 2021 daga Naira tiriliyan 1.4 zuwa Naira tiriliyan 1.56.

Wannan ne kudin da aka lafta wa hukumar ta kwastam mai maganin fasa-kauri, kafin a rage a adadin a dalilin annobar Coronavirus ta barke a kasashe.

KU KARANTA: Alkali ya yi hukunci a kan kammala rajistar NIN a ranar 6 ga watan Afrilu

Yanzu kwamiti ya sake yin sama da kudin a lokacin da shugaban hukumar kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya ya zauna da ‘yan majalisar wakilai.

Kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, Hameed Ali ya kare kasafin kudin hukumar ne a ranar Talata, 30 ga watan Maris, 2021, a babban birnin tarayya Abuja.

Kanal Ali mai ritaya ya koka da cewa yarjejeniyar kasuwancin da Najeriya ta shiga da kasashen Afrika da kungiyar WTO ya rage masu kudin da su ke samu.

Bayan haka hukumar kwastam ta bada shawarar a haramta kawo duk wata mota da aka yi amfani da ita na tsawon sama da shekaru bakwai a kasar waje.

Gwamnatin Najeriya ta na neman haramta kawo motar da ta shekara 7 a Duniya
'Yan Majalisar Tarayya Hoto: House of Reps
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gobara ta tashi a kasuwar Katsina yayin da mutane su ke barci

Shugaban kwamitin, Leke Abejide, ya ce ba za a rage burin da aka ci a kan kwastam ba ganin yadda jami’anta su ka tatsi kudi a lokacin da ake zaman kulle.

Honarabul Abejide ya ce an kara kudin da ake hari tun da an kara VAT, ‘dan majalisar ya ce ba za su so su samu matsala da Ali wajen amince wa da kasafin ba.

A ranar Litinin kun ji cewa ana zargin wasu kudin ribar da aka samu na cinikin mai, har kusan Naira Biliyan 4 sun yi batar-dabo daga asusun CBN Najeriya.

Sanatocin Najeriya sun ce ya zama dole Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi mata bayanin yadda Dala miliyan 9.5 su ka yi kafa kafin ranar Alhamis dinnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel