Yanzu-Yanzu: Bidiyon Yadda Aka Tarbi Buhari a Birnin Landan

Yanzu-Yanzu: Bidiyon Yadda Aka Tarbi Buhari a Birnin Landan

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Landan domin duba lafiyarsa

- Ana sa ran shugaban na Nigeria zai yi makonni biyu ne a kasar ta Birtaniya

- Kafin ya baro Nigeria, Buhari ya gana da manyan hafsoshin sojojin Nigeria a ranar Talata

Jirgin Shuagan Nigeria, Muhammadu Buhari ta isa birnin Landan da ke kasar Birtaniya inda zai ga likitocinsa kamar yadda hadiminsa @bashirahmaad ya sanar a Twitter.

A yau Laraba 30 ga watan Maris ne shugaban na Nigeria ya baro birnin tarayya Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.

DUBA WANNAN: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Yanzu-Yanzu: Bidiyon Yadda Aka Tarbi Buhari a Birnin Landan
Yanzu-Yanzu: Bidiyon Yadda Aka Tarbi Buhari a Birnin Landan. Hoto: @Bashirahmaad
Asali: Twitter

Kafin zuwansa, shugaban kasar ya gana da manyan hafsoshin sojojin kasar inda ya zaburar da su da su gaggauta wurin kawar da bata gari da yan bindiga da ke adabar kasar.

Shugaban kasar zai shafe makonni biyu ne a kasar na Landan kamar yadda hadiminsa garba Shehu ya sanar.

Tun da ya hau kan mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tafiye-tafiye da masu yawa zuwa kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Amma wannan shine karonsa na farko zuwa Birtaniya tun bayan barkewar annobar COVID-19 da ta bazu a kasashen duniya.

KU KARANTA: An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

Ga bidiyon saukar shugaban kasar a birnin Landan.

A yayin da wasu yan Nigeria ke ganin bai dace shugaban ya cigaba da zuwa kasashen waje don ganin likitoci ba, fadar shugaban kasar ta ce ba sabon abu bane a wurinsa domin ya kwashe kimanin shekaru 30 yana zuwa ganin likitocin.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164