Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin soji, mutum 9 sun sheka lahira a Dabanga
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojin kasar Kamaru dake Dabanga
- Kamar yadda aka gano, sun kai farmakin ne da farkon dare inda suka dinga ruwan wuta
- An rasa rayukan 'yan Boko Haram 6, farar hula 3 da kuma sojan kasar Kamaru daya
Mayakan ta'addancin na Boko Haram shida, fararen hula uku da wani sojan kasar Kamaru sun mutu a ranar Asabar, 27 ga watan Maris, a harin daren da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai sansanin sojoji dake Dabanga, yankin arewacin Kamaru.
Kamar yadda ganau ya sanar, mayakan dauke da miyagun makamai sun isa sansanin a motoci da babura yayin da suka ga dare ya fara yi.
"Sun wuce bayan mun dawo daga Masallaci. A zatonmu dakarun soji ne dake aikin sintirin da suka saba," Adamou Adoum, daya daga cikin 'yan sa kan yankin ya sanar.
KU KARANTA: Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai
KU KARANTA: Doka da tsoron Allah ne jagororinmu, sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa
Kamar yadda jaridar HumAngle ta ruwaito, "Wasu matasa ne suka sanar da mu cewa wadannan jama'an ba dakarun taimakon gaggawa bane (BIR)."
"Hakan ce tasa muka gane 'yan Boko Haram. Kowa ya tsere tare da shigewa gida. Daga nan ne muka ji karar bindiga sannan muka fara fitowa domin boyewa a daji," yace.
A yayin harin, 'yan Boko Haram din sun dinga ragargazar sansanin BIR.
"Dakarun sojin Kamaru da wasu jami'an tsaron hadin guiwa (MNJTF) sun gaggauta kaddamar da ruwan wuta bayan sun gano su waye mayakan, lamarin da yasa 'yan Boko Haram suka tsere," wani ganau ya sanar da HumAngle
“Daga bisani, an kashe 'yan Boko Haram 6, farar hula 3 da soja 1 yayin da wadanda suka kai harin suka tsere tare da barin ababen hawansu da makamansu."
Majiyoyin yankin sun ce tuni zaman lafiya ya dawo Dabanga kuma wadanda suka tsere daji suka koma gidajensu.
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tace a ranar Lahadi jami'anta sun bankado wani yukurin garkuwa da aka yi da wasu mutum biyar kuma ta ceto su.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.
"Rundunar na sanar da jama'a cewa tana matukar kokari wurin tabbatar da ta shawo kan matsalar 'yan bindiga, garkuwa da mutane, satar shanu da fashi da makami a jihar kuma tana samun nasarori," Jalige yace.
Asali: Legit.ng