Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno

Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno

- Zakakuran sojojin Najeriya na cigaba da samun nasarori a yaki da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas

- Horarrun sojojin cikin kwanakin nan suka sheke wasu mayakan Boko haram a jihar Borno

- An halaka 'yan ta'addan ne bayan an kama su suna dasa bama-bamai a kan hanyar wucewar sojojin Najeriya

Zakakuran sojojin sashi na 1 karkashin rundunar Operation Lafiya Dole sun halaka wasu mayakan ta'addanci na Boko Haram a hanyar Njimia dake Alafa, kusa da dajin Sambisa dake jihar Borno.

Kwamandan runduna ta musamman ta 21 dake Bama, Waidi Shayibu, ya jagoranci aikin.

An halaka 'yan ta'addan yayin da suka dasa abubuwa masu fashewa a hanyar da dakarun sojin ke bi.

Jami'in sirrin da ya bukaci a boye sunansa ya sanar da PR Nigeria cewa 'yan ta'adda kadan ne suka tsere da miyagun raunika.

KU KARANTA: Okorocha ya sha mugun duka a hannun basarake a cikin jirgin sama

Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno
Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Doka da tsoron Allah ne jagororinmu, sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa

A kalamansa:

"Kamar yadda muka saba hadin guiwa tsakanin dakarun sojin sama da na kasa, rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukan mayakan Boko Haram a wasu hanyoyi.

"A lokacin da muka samu tabbaci, dakarunmu sun yi lambo yayin da suka hango su sannan suka bi su da ruwan wuta. An samu gawawwakin 'yan ta'adda 7, bindigoginsu, bindigar harbo jirgin sama da babura.

"An samu wasu abubuwa masu fashewa a gefen tituna kuma sojojin sun lalata su."

A wani labari na daban, a kokarin tabbatar da binciken da ya dace tare da damke masu hannu a harin da aka kaiwa gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya tura gagarumar rundunarsa daga Abuja zuwa Binuwai karkashin shugabancin DCP Abba Kyari.

IGP Adamu ya bukaci rundunar da su nuna kwarewarsu da hazakarsu yayin bincike, jaridar Leadership ta bayyana.

A yayin tabbatar da sahihancin labarin, kakakin rundunar 'yan sandan, Frank Mba yace, "Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya kafa gagarumar rundunar bincike domin cigaba da aiki kan rahoton hari da yunkurin kashe Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom. Rundunar ta isa garin Makurdi."

Source: Legit

Online view pixel