Sanatoci sun ba Gwamnan CBN, Emefiele kwana 3 ya zo gabansu a kan zargin bacewar Biliyan 4

Sanatoci sun ba Gwamnan CBN, Emefiele kwana 3 ya zo gabansu a kan zargin bacewar Biliyan 4

- Kwamitin Majalisa ya na binciken wasu kudi da ake zargin sun sulale a CBN

- Majalisar Dattawa ta kira gwamnan CBN ya yi bayanin inda kudin su ka shiga

- Wadannan kudi sun kai fam $9.5m, kimanin Naira biliyan 4 a kudin Najeriya

A ranar Litinin ne majalisar dattawan Najeriya ta ba gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, wa’adin sa’o’i 72 domin ya bayyana a gabanta.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa ‘yan majalisar su na neman Godwin Emefiele ne kan zargin bacewar Dala miliyan 9.5 daga asusun Najeriya.

Wadannan makudan kudi sun yi kafa daga cikin asusun ribar da ake samu daga kasuwancin mai.

KU KARANTA: Ya kamata a rika ba mata mukamai, sun fi maza kwakwalwa - Minista

Kwamitin binciken kudi na majalisar dattawa ta bakin shugabanta, Sanata Matthew Urhoghide, ta na zargin akwai badakala a aikin da CBN ta ke yi.

Matthew Urhoghide ya zargi babban bankin da boye yadda ake gudanar da sha’anin kasuwancin, tun daga wajen ajiye uwar kudi da ribar da aka samu.

Sanata Urhoghide ya ce akwai abubuwan da ake bukatar Godwin Emefiele ya zo gaban majalisa ya yi karin bayani domin a san inda kudin su ka shiga.

Majalisar dattawan ta ba gwamnan na CBN tsawon kwanaki uku kacal ne domin ya hallara a gabanta.

Sanatoci sun ba Gwamnan CBN, Emefiele kwana 3 ya zo gabansu a kan zargin bacewar Biliyan 4
Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya nada sababbin Darektoci 5 a hukumar NASENI

A makon da ya gabata, Sanatoci sun aika wa jami’an bankin CBN sammaci a dalilin zargin da ake yi na cewa ribar kudin cinikin mai da aka adana, sun yi dabo.

A zaman da majalisar tarayya ta yi a jiya ranar Litinin, daga Godwin Emefiele har jami’an CBN da aka gayyata, babu wanda ya amsa gayyatar Sanatocin kasar,

‘Yan majalisar sun dogara ne da rahoton mai binciken kudi na kasa ya fitar, inda ya ce bai san inda $9.5m na ribar PPT da asusun kudin kasar waje su ka shiga ba.

Rahotanni su na zuwa mana cewa Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na jagorantar zaman majalisar tsaro a cikin fadar Aso Villa yanzu haka.

Farfesa Yemi Osinbajo, Boss Mustapha, Ministan tsaro, shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Babagana Monguno da duka hafsoshin tsaro su na wajen taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel