Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun

- Wasu yan daba sun kaiwa OLateju Adunni, hadimin ministan harkokin cikin gida, Ogbenni Rauf Aregbesola hari a Oshogbo jihar Osun

- Shaidar gani da ido, Rasheed Ropo, ya ce yan daban sun iso ne cikin mota mai cin mutum 18 suka afka musu da duka

- Rasheed, tsohon kansilar karamar hukumar Odu-Odin ya ce daga bisani yan sanda sun zo sun kwantar da tarzomar

Bayan lamban yabo da aka bawa ministan harkokin cikin gida, Mr Rauf Aregbesola wasu ƴan daba a daren jiya Lahadi sun kaiwa ɗaya daga cikin hadimansa, Olateju Adunni da abokansa hari a wurin casu a Oshogbo, Vanguard ta ruwaito.

A cewar shaidan ganin ido, Rasheed Ropo, ƴan daban sun afka wurin shaƙatawa inda ɗan majalisar jihar Osun, Hon. Taofeek Badamasi ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa cikin mota mai ɗaukan mutum 18.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

Rasheed, tsohon kansila a ƙaramar hukumar Odo-Otin ya ce Teju da Hon Taofeek dan majalisa mai wakiltar Oshogbo a majalisar suke nema.

"Sun tafi wurin biki ne na murnar zagayowar ranar haihuwar Hon Taofeek Badmus, ɗan majalisa mai wakiltar Oshogbo. Badmus ya gayyace mu. Mun hadu da wasu yan majalisa kamar Hon Festus Komolafe, Hon Babatunde Desmond Ojo a wurin. Mun dauki tsawon lokaci muna cin abinci da shan abubuwan sha.

"Mun dab da tafiya, sai muka ga wasu ƴan daban suna saukowa daga Bus mai cin mutum 18. Mun koma cikin wurin cin abincin da gaggawa.

"Ƴan daban sun biyo mu ciki suna ihu suna cewa, Shine Teju, Shine Teju. Suka fara dukansa. An naushi Hon. Taofeek kafin ya samu ya tsere nan take. Yayin da yan daban ke dukan Teju, ni da Kehinde Adedeji, Wale Omolala da Dare Ogundotun munyi yunkurin cetonsa.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

"Suka juyo kanmu suka fara kai wa mutane da dama hari. An kai wa Alhaji 'Simple' yayan Sanata Ajibola Basiru mai wakiltar Osun ta Tsakiya hari. An sare shi da adda a kai kafin ya tsere," in ji shi.

Amma wata majiya daga wurin da aka yi da taron ta ce ba a kai wa kowa hari a cikin wurin ba amma anyi faɗa a waje.

Majiyar ta ce ƴan sanda sun zo cikin gaggawa sun kwantar da tarzomar.

Duk da cewa Hon Taofeek bai amsa wayarsa ba ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ya tsere daga wurin ba tare da wani rauni ba.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel