Okorocha ya sha mugun duka a hannun basarake a cikin jirgin sama

Okorocha ya sha mugun duka a hannun basarake a cikin jirgin sama

- An kwashi ƴan kallo a cikin jirgin sama bayan wani babban basarake ya kaiwa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha farmaki

- Basaraken ya daga sandarsa ne yayi kokarin rafka wa Rochas sakamakon wata jiƙaƙƙiya da suke da ita tun yana kan mulki

- Kamar yadda ganau suka tabbatar, al'amarin ya faru ne a tashar jirgin saman Sam Mbakwe dake Owerri a ranar Lahadi

An samu wata ƴar hayaniya a cikin jirgin sama na tashar jirgin Sam Mbakwe dake Owerri a ranar Lahadi tsakanin tsohon basarake, Eze Cletus Ilomuanya na jihar Imo da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha.

Ganau sun ce Ilomuanya yana zaune hankali kwance kafin isowar Okorocha, The Nation ta wallafa.

Zuwansa ke da wuya yayi gaggawar miƙewa don rafka masa sandar da yake tafiya da ita cikin hanzari da harzuƙa.

Basaraken ya yi yunƙurin yi wa tsohon gwamnan baƙin duka akan wulaƙanta shi da yayi lokacin yana kan karagar mulki.

KU KARANTA: Rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, Idris Deby

Basarake ya kaiwa Okorocha farmaki a jirgin sama, ya nemi masge shi da sandarsa
Basarake ya kaiwa Okorocha farmaki a jirgin sama, ya nemi masge shi da sandarsa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram na horar da makiyaya tare da karbar shanu a matsayin haraji, Rahoto

Al'amarin ya fara ne kamar wasa kafin basaraken ya kai masa ɓazga yana daka masa tsawa akan ya daina shiga harkarsa da ta mutanen Orlu.

Sai da jami'an jirgin saman suka yi ca a kansu kuma akayi gaggawar dakatar da Ilomuanya daga cigaba da dukan Okorocha da sandarsa don samar da maslaha.

Sai dai Okorocha ko tankawa bai yi ba kuma ya nuna halin ko in kula tare da gaggawar canja wurin zama koda Ilomuanya yake hayagagagar ya daina shiga harkar mutanen Orlu.

Ilomuanya yana daya daga cikin sarakunan da Okorocha ya tube wa rawani a ranar 6 ga watan Yunin 2014, bayan cire shi da aka yi daga shugaban sarakunan tun kafin lokacin.

A wani labari na daban, shugaban ƙasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayar da tabaccin cewa rundunar sojin haɗaka zasu iya kawo ƙarshen ta'addancin Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Chadin a ranar Asabar ya tabbatar da hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati a fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ziyarar kwana daya da ya kawo.

Shugaban Chadin ya cigaba da bayyana yadda ta'addanci yake cigaba da ciwa kowa tuwo a ƙwarya musamman a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel a Afirika saboda MNJTF basu fara aiki a wuraren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng