Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai

Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai

- Tawagar DCP Abba Kyari ta dira jihar Binuwai domin tsamo wadanda suka kaiwa Gwamna Ortom hari

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da isar tawagar garin Makurdi dake jihar Binuwai domin cigaba da bincike

- Kamar yadda Frank Mba, kakakin rundunar ya sanar, IGP ya bukaci tawagar ta hada kai da 'yan sandan jihar domin bincike

A kokarin tabbatar da binciken da ya dace tare da damke masu hannu a harin da aka kaiwa gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya tura gagarumar rundunarsa daga Abuja zuwa Binuwai karkashin shugabancin DCP Abba Kyari.

IGP Adamu ya bukaci rundunar da su nuna kwarewarsu da hazakarsu yayin bincike, jaridar Leadership ta bayyana.

A yayin tabbatar da sahihancin labarin, kakakin rundunar 'yan sandan, Frank Mba yace, "Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya kafa gagarumar rundunar bincike domin cigaba da aiki kan rahoton hari da yunkurin kashe Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom. Rundunar ta isa garin Makurdi.

KU KARANTA: Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi

Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai
Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai. Hoto daga @Leadership
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram na horar da makiyaya tare da karbar shanu a matsayin haraji, Rahoto

"Tawagar da ta samu jagorancin DCP Abba Kyari, ta hada da jami'an FIB da sauran kwararru da suka kasance zakaru wurin binciken masu laifi.

"Ana tsammanin tawagar za ta dasa daga kan bincike da aka fara kan lamarin."

Tawagar za ta binciki duk wani lungu da sako na harin tare da tabbatar da ta bankado duk wasu masu alaka da lamarin.

"Ana tsammanin za su yi aiki tare da rundunar 'yan sandan jihar Binuwai da sauran jami'an tsaro wurin tabbatar da sun yi aiki mai kyau."

A wani labari na daban, Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya dora laifin rashin tsaron Najeriya a kan masu fadi a ji a kasar nan, Jaridar The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne yayin jawabin yayen dalibai karo na 34 na jami'ar Kalaba. Amaechi yasa masu fadi a ji a harkar siyasar Najeriya sun yi watsi da talakawa wanda hakan yasa talakawan suka fada miyagun laifuka.

"Ba zai yuwu a ce mun kasa gane abinda masu fadi a ji a kasar nan suka samar ba a fannin tsaron kasar nan ba. A wasu sassan kasar nan, masu fadi a ji a fannin siyasa sun kasa sauke nauyin dake kansu na ilimantar da 'ya'yan talakawa."

Source: Legit

Online view pixel