Gagarumar gobara ta lashe kasuwar doya ta Namu dake Filato
- Ibtila'in gobara ya fada wa kasuwar doya ta Namu dake karamar hukumar Qu'an Pan ta Filato
- Mummunar gobarar ta tashi ne da daren Lahadi inda ta lamushe kayan abinci na miliyoyin naira
- Wani ganau ba jiyau ba, ya tabbatar da cewa har a halin yanzu ba a san musabbabin gobarar ba
Gagarumar gobara ta tashi a kasuwar doya inda ta cinye kayan abinci na miliyoyin naira a kasuwar Namu dake karamar hukumar Qu'an Pan ta jihar Filato.
Wani ganau ba jiyau ba ya sanar da cewa har yanzu ba a san musabbabin gobarar da ta tashi a daren Lahadi ba.
Wani mazaunin yankin, Kabiru Buba, ya ce sama da manoma 100 ne gagrumar gobarar ta shafa.
KU KARANTA: Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna
KU KARANTA: Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi
A don haka Buba yayi kira ga gwamnati a kowanne mataki da ta kawowa manoman dauki.
Har ila yau, sanata mai wakiltar mazabar Filato ta kudu, Nora Dadu'ut, ya jajantawa wadanda lamarin ya shafa tare da basaraken yankin, Long Jan na Namu, Safiyanu Allahnana.
"Ina jaje ga dukkan jama'ar Namu a kan wannan ibtila'in," Dadu'ut yace a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.
"Tun bayan da naji aukuwar lamarin, ban shiga natsuwa ba. na fada tsananin damuwa. Ina fatan Ubangiji ya sauyawa wadanda lamarin ya shafa da mafi alheri," yace.
Sanatan yayi kira ga gwamnati da sauran 'yan Najeriya da su basu tallafi.
A wani labari na daban, shugaban ƙasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayar da tabaccin cewa rundunar sojin haɗaka zasu iya kawo ƙarshen ta'addancin Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ƙasar Chadin a ranar Asabar ya tabbatar da hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati a fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ziyarar kwana daya da ya kawo.
Shugaban Chadin ya cigaba da bayyana yadda ta'addanci yake cigaba da ciwa kowa tuwo a ƙwarya musamman a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel a Afirika saboda MNJTF basu fara aiki a wuraren ba.
Asali: Legit.ng