Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna

Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tace jami'anta sun bankado wani yunkurin sace mutane 5 kuma sun ceto su

- A ranar Lahadi ne 'yan bindiga suka rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari tare da yunkurin sace fasinjojin wata motar haya

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, yace jami'ansu sun ragargaji 'yan bindigan wurin karfe 12 na rana

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tace a ranar Lahadi jami'anta sun bankado wani yukurin garkuwa da aka yi da wasu mutum biyar kuma ta ceto su.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

"Rundunar na sanar da jama'a cewa tana matukar kokari wurin tabbatar da ta shawo kan matsalar 'yan bindiga, garkuwa da mutane, satar shanu da fashi da makami a jihar kuma tana samun nasarori," Jalige yace.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da ganye launin zinari

Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna
Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki

Kamar yadda yace, "A ranar 26 ga watan Maris wurin karfe 12 na rana labarai suka same mu na cewa 'yan bindiga 10 dauke da makamai sun rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari kuma suna kokarin kwashe fasinjojin wata mota kirar Golf mai lamba DKA 539 TU dake tafiya Birnin Gwari zuwa Kaduna.

"Daga samun rahoton, rundunar sintirin dake yankin Buruku ta fara aiki. Sun yi musayar wuta da 'yan bindigan kuma cike da nasara suka fatattakesu da miyagun raunika tare da ceto mutanen.

"A halin yanzu jami'an tsaron na tsananta neman 'yan bindigan don cafke su," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan yace tuni wadanda aka yi yunkurin sacewan suka sadu da 'yan uwansu.

A wani labari na daban, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da 'yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jihar Yobe inda 'yan Boko Haram ke horar da makiyayan dabarun yaki.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace 'yan ta'addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.

An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel