Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hallartar Casu da 'Yahoo Boy' Ya Haɗa a Legas

Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hallartar Casu da 'Yahoo Boy' Ya Haɗa a Legas

- Kimanin mutane 50 ne aka ruwaito sun rasu bayan hallartar casun birthday a jihar Legas

- Wani dan damfara ta intanet wato Yahoo Boy ne ya hada casun a Legas a cewar rahotanni

- A cewar wani @pelumiawotedu a Twitter, lamarin ya faru ne a Unguwar Alagboke Akute a Legas

Wani matashi a dandalin sada zumunta ya yi alhinin rashin abokansa bayan mutane 50 sun mutu a wani yanayi mai daure kai bayan hallartar casun da wani da ake zargin 'Yahoo boy' ne ya hada.

Lamarin mai ban tsoro ya faru ne a Alagbole Akute, jihar Legas a cewar wani mai amfani da Twitter @pelumiawotedu.

Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hallartar Casu da 'Yahoo Boy' Ya Haɗa a Legas
Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hallartar Casu da 'Yahoo Boy' Ya Haɗa a Legas. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

Wani matashi mai damfara ta intanet 'yahoo boy' a cewar majiyoyi a dandalin sada zumunta, ya shirya gagarumin casu domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa Lahadi biyu da suka gabata inda abokansa 50 suka hallarci taron.

Sai dai dukkansu 50 sun mutu cikin wani yanayi mai daure kai bayan hallartar casun da aka kashe dare ana yi.

Wani mai amfani da Twitter @ysquare_r shima ya yi ikirarin makwabcinsa ta rasa abokinta, danta da wani yaro sakamakon hallartar casun. Ya kara da cewa wani mutum a layinsu da abokansa hudu da suka hallarci casun suma duk sun mutu.

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

A cewar @ysquare, a lokacin da ya wallafa rubutun, mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya kuma akwai yiwuwar wasu sun mutu bayan su.

Ga abinda ya wallafa a nan kasa:

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: