Shugabannin Kiristoci a Legas Sun Ce Suna Son Musulmi Ya Zama Gwamna a 2023

Shugabannin Kiristoci a Legas Sun Ce Suna Son Musulmi Ya Zama Gwamna a 2023

- Shugabannin Kiristoci a jihar Legas sun ce ya kamata musulmi ya zama gwamna a shekarar 2023

- Fasto Sam Ogedengbe, Sakataren kungiyar shugabannin kiristoci da masu wa'azi na Legas ne ya bayyana hakan

- Ogedengbe ya ce suna cikin wadanda suka nemi a bawa kirista gwamnan bayan mulkin Fashola, kuma sun samu don haka yanzu lokacin musulmi ne

Shugaban Kungiyar Shugabannin Kiristoci da Masu Wa'azi, Fasto Sam Ogedengbe ya ce ya kamata musulmi ya zama gwamnan jihar Legas a shekarar 2023 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne a karshen mako a Abule-Egba, Legas yayin taron kungiyar na shekara-shekara da bikin ban godiya.

Lokaci Ya Yi Da Kamata Musulmi Ya Karbi Mulki a Legas, Shugabannin Kiristoci
Lokaci Ya Yi Da Kamata Musulmi Ya Karbi Mulki a Legas, Shugabannin Kiristoci. @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

Ogedengbe, wanda shine shugaban cocin Overcomers Pentecostal Prayer Church, Abule Egba, Legos ya ce baya da haufi cewa gwamnan Legas da za a zaba a 2023 zai kasance musulmi ne.

Tsohon hadimin na gwamnan Legas kan harkokin addinin kirista ya ce yana daga cikin wadanda suka nema a bawa kirista gwamna bayan mulkin Babatunde Fashola, hakan yasa aka samu tsohon gwamna Akinwunmi Ambode da gwamna mai ci yanzu Babajide Sanwo-Olu.

Ya ce maganan gaskiya shine shi da sauran shugabannin kirista ba za su zama butulu ba don haka za su goyi bayan ganin musulmi ya zama gwamna.

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

"Mu shugabannin kirista mun goyi bayan gwamnatoci tun 1999, amma za mu tabbatar wanda zai gaji Sanwo-Olu musulmi ne saboda adalci da dai-daito," in ji Ogedengbe.

Gwamna Sanwo-Olu, wadda ya samu wakilcin mashawarcinsa na musamman kan harkokin addinin kirista, Rev. Bukola Akindele ya ce ya kamata kowa ya mara wa gwamnati mai ci yanzu baya don sake gina jihar musamman bayan annobar COVID-19 da zanga-zangar EndSARS.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel