Za'a bankaɗo ma Najeriya da ƙasashen Afrika allurar Rigakafin COVID19 ta Johnson & Johnson guda 400 Miliyan

Za'a bankaɗo ma Najeriya da ƙasashen Afrika allurar Rigakafin COVID19 ta Johnson & Johnson guda 400 Miliyan

- Africa ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Johnson & Johnson kan samar da rigakafin korona kusan 400 miliyan ga ƙasashen Afrika

- Ƙungiyar amintattu kan siyan Allurar rigakafi a nahiyar AVATT ce ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin.

- Za kuma a fara rarraba allurar rigakafin a cikin wannan shekarar da muke ciki 2021.

Ƙungiyar dake kula da siyan allurar rigakafi a Africa (AVATT) ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Johnson & Johnson kan kawo rigakafin korona 400 miliyan nahiyar.

Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa za'a kaima kowacce kasa daga ƙasashen Africa 55, kuma za'a fara aikin ne a shekarar da muke ciki 2021, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jihar Kano da Legas na da matukar muhimmanci ga Najeriya, Inji Asiwaju Bola Tinubu

Da farko za'a fara kawo rigakafin guda 200 miliyan kafin daga bisani a ƙaro guda 180 miliyan zuwa ƙasashen nahiyar ta Africa.

Johnson & Johnson sun bayyana cewa kamfanin su dake ƙasar South Africa zai ɗauki nauyin rarraba rigakafin zuwa ƙasashen kuma kamfanin zai taimaka wajen samar da rigakafin.

Za'a bankaɗo ma Najeriya da ƙasashen Africa allurar Rigakafin COVID19 ta Johson & Johnson guda 400 Miliyan
Za'a bankaɗo ma Najeriya da ƙasashen Africa allurar Rigakafin COVID19 ta Johson & Johnson guda 400 Miliyan Hoto: @DigicommsNG
Source: Twitter

Lokacin da yake magana kan cigaban da aka samu, shugaban ƙasar South Africa, Cyril Ramaphosa, wanda shine shugaban AVATT ya ce:

"Wannan yarjejeniyar zata kafa tarihi, kuma mataki ne mai kyau wajen kare rayuwar yan nahiyar Africa. Kuma wannan babban dalili ne dake nuni da haɗin kan ƙasashen mu na Africa."

KARANTA ANAN: Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra

Shugaban kamfanin Johnson & Johnson, Alex Gorsky, ya bayyana cewa yarjejeniyar da kamfanin suka yi da shirin COVAX zai matuƙar taimakawa wajen fatattakar wannan cutar a nahiyar.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata AVATT ta ƙaddamar da shirin ta na samar da rigakafin korona ga kasashen Africa.

Tun wannan lokacin, AVATT wadda shugaban South Africa ke jagoranta tare da ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) suka amince da shirin COVAX.

Shirin na COVAX ya samar da allurar rigakafin korona ta Astrazeneca ga ƙasashen dake nahiyar Afrika.

A wani labarin kuma Likitoci zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba

Ƙungigar Likitocin ƙasar nan NARD ta bayyana cewa zata tsunduma cikin yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya su haƙƙokin su ba

Ƙungiyar ta baiwa gwamnati wa'adi zuwa ƙarshen watan Maris ta yi abinda ya kamata ko su shiga yajin aiki.

Source: Legit

Online view pixel