Abin da Buhari, Gwamnoni, Shugabannin Majalisa ke fada yayin da Tinubu ya isa shekara 69

Abin da Buhari, Gwamnoni, Shugabannin Majalisa ke fada yayin da Tinubu ya isa shekara 69

- Fitaccen ‘dan siyasa, Asiwaju Bola Tinubu ya cika shekara 69 a Duniya a yau

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi, ya taya Tinubu murna

- Shugabannin Majalisar Tarayya duk sun fito su na yabon babban Jigon na APC

Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila sun taya Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekara 69.

Haka zalika gwamnonin jihohin kasar nan sun fito su na taya babban ‘dan siyasar murnar zagayowar rannan haihuwarsa a ranar Litinin, 29 ga watan Maris, 2021.

Shugaban kasa ya fitar da jawabi ne ta bakin babban mai magana da yawunsa, Garba Shehu.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Kano ya kai Bola Ahmed Tinubu fadar Sarki Bayero

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana Asiwaju Bola Tinubu a matsayin daya daga cikin manyan tubulin jam’iyyar APC, ya ce tsohon gwamnan ya daura da-dama a kan hanya.

Muhammadu Buhari ya yi addu’a ga Ubangiji ya ba jigon na APC karfin lafiya, tare da bayyana irin kokarin da ya yi wajen ganin jam’iyyar APC ta tsaya a kan kafafunta.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ta bakin wani hadiminsa, Ola Awoniyi, ya bayyana tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu a matsayin mai cikakken kishin kasa.

Jawabin Sanatan Lawan ya ke cewa: “Ina taya Mai girma, Bola Tinubu, murna a wannan rana ta farin ciki. Shugaban shugabanni, kwararren ‘dan siyasa, gogaggen mai mulki."

KU KARANTA: Ba za ayi maganar 'Yan siyasa ba tare da Tinubu ba - Sanwo Olu

Abin da Buhari, Gwamnoni, Shugabannin Majalisa ke fada yayin da Tinubu ya isa shekara 69
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban majalisar kasar ya ce an shafe shekaru kimanin 30 ana gurza wa da Tinubu a fagen siyasa.

Haka zalika Sanata Ovie Omo-Agege ya fitar da jawabi ya na taya Jagaban of Borgu murnar kara shekara a Duniya, ya ce shi ne silar maida jihar Legas abin da ta zama a yau.

Shi kuwa Femi Gbajabiamila ya yabi jajircewa da tsayawa tsayin dakan ‘dan siyasar wajen ganin damukaradiyya ta kafu, ya yi kira ga sauran ‘yan siyasar kasar su yi koyi da shi.

A karshen makon nan kun samu rahoto cewa wani faifan bidiyo da ya fito, ya nuna jagoran jam'iyyar APC na kasa ya yi turgude, ya jawo surutu a shafukan sada zumunta.

Saura kiris tsohon gwamnan na jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya fadi war-was a kasa yayin da ya shiga dakin taron Arewa House da ke garin Kaduna inda aka shirya lacca.

Asali: Legit.ng

Online view pixel